September 18, 2026

Gwamna Raɗɗa Ya Kaddamar Da Cibiyar Zaman Lafiya Da Sauyin Yanayi a Katsina

IMG-20260612-WA0020

 

Daga Wakilinmu

Gwamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da cibiyar zaman lafiya da sauyin yanayi da zata taimaka wajen karfafa zaman lafiya.

Haka kuma kirkirar cibiyar na da nufin samar da ƙyawawan hanyoyin yaki da sauyin yanayi da bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’ummomin da ke fuskantar ƙalubale a jihar Katsina

An ƙaddamar da wannan cibiya ne a gaban jakadun ƙasashen Norway da Jamus da kungiyoyin raya ƙasa da mambobin majalisar zartarwa a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

An ƙaddamar da cibiyar ne a ranar Alhamis tare da halartar jakadun ƙasashen Norway da Jamus, wakilan ƙungiyoyin raya ƙasa, mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar Katsina, ’yan majalisa, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki.

Ita dai wannan cibiya an kafa ta ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Katsina da shirin raya ƙasashe na majalisar dinkin duniya ƙarƙashin (UNDP) da gwamnatin ƙasar Norway da nufin haɗa ayyukan zaman lafiya da noma da fasahar zamani da kuma koyon sana’o’i domin amfanin al’umma

Tunda farko da yake jawabi gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa samar da cibiyar zai buɗe wani sabon shafi na tallafawa mata da matasa ta hanyar samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

“Abinda nake kowa ya gane shi ne, wannan cibiya ta yi daidai da manufofin gwamnatina na samar da cigaba mai ɗorawa a yankunan da matsalar tsaro ta yi wa kamun kazar kiki tare kawo sauyi mai ma’ana

Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa cibiyar tana ɗauke da muhimman kayayyakin aiki da suka haɗa da tashar lura da yanayi da gonakin noman zamani, cibiyar sasanta rikice-rikice, dakunan koyon fasahar sadarwa da cibiyoyin koyon sana’o’i.

Shima da yake jawabi a lokacin taron buɗe cibiyar, manaja mai kula da wurin, Muhammad Aliyu ya yi bayanin cewa an samar da wannan cibiya ne domin magance matsalolin sauyin yanayi da rikice-rikice da ke faruwa a tsakanin al’umma.

A cewar sa, wannan cibiya tana ɗauke ne da gonakin zamani da wuraren sasanta rikice-rikice da inda za a shayar da dabbobi da hanyoyin samar da makamashi da kuma wani sashe na fasahar zamani

“Wannan cibiyar tana Horos da Mata da matasa akan sana’o’i daban-daban da suka haɗa da dinki da gyaran jiki da kwalliya da sake sarrafa robobi tare da samar da gawayi domin yin grike-girke.” Inji shi

Muhammad Aliyu ya ƙara da cewa zuwa yanzu waɗanda suka amfana da shirye-shirye wannan cibiya akwai masu koyon aikin Noma na zamani wanda har sun fara samun kuɗaɗen shiga, ya yin da mata 100 za su samu horo akan sana’o’i daban-daban.

About The Author