September 19, 2026

Matsalar Tsaro: Manoma Sun Koma Gonakin Su A Katsina – Dikko Raɗɗa 

FB_IMG_1780577428431

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa an samu tsaro a ƙaramar hukumar Jibia wanda haka tasa Manoma sun koma gona.

 

Dikko Raɗɗa ya bayyana haka a lokacin bikin ƙaddamar da gidaje 152 da hukumar UNDP hadin gwiwa da gwamnatin Katsina suka ginawa mutanen da bala’in ‘yan bindiga ya raba da muhallin su a karamar hukumar Jibia.

 

Haka kuma ya bayyana cewa yanzu an kwashe fiye da shekara ɗaya ba a kai hari ko sace wani ba a ƙaramar hukumar ta Jibia saboda zaman lafiyar da aka samu.

 

Gwamna Raɗɗa ya ƙara da cewa duk kasuwannin da suke rufe yanzu an buɗe su, yara sun koma makaranta, sannan farashin kayan abinci ya sauka kwarai da gaske.

 

Kazalika gwamna Raɗɗa ya yi kira ga al’umma da su kasance masu lura da lamarin tsaro wanda ya ce abu ne da ya shafi kowa da kowa ba gwamnati kaɗai ba.

 

“Tsaro ba aikin gwamnati bane kawai, ana iya samar da shi a kowane gida, a kowace kasuwa, a kowane masallaci da kuma mujami’a” inji shi

 

Sannan gwamnan ya yi kira ga ‘yan bindiga da su zo su rungumi zaman lafiya a zauna da su cikin al’umma kamar kowa, bisa sharadin ajiye makaman su.

 

“Har yanzu kofar sasanshi a buɗe take ga waɗanda suka yarda za su ajiye makamai, suna san su dawo cikin mutane su yi rayuwa kamar kowa cikin iyalan su, wuri bai kure masu ba.” Inji shi

About The Author