September 16, 2026

Sharuɗɗa Biyu Na Zama Da Dakta Mustapha Inuwa A Siyasa

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Daraktan yaɗa labarai na ofishin Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Aliyu Yar’adua ya bayyana wasu sharruɗa guda na zama tare da Mustapha Inuwa a siyasa.

Abdullahi Aliyu ya faɗi haka ne lokacin da ya wakilci Dakta Mustapha Inuwa a taron da kungiyar nan mai fafutukar kafa demokradiyya mai dorewa a jihar katsina (KDF) ka shirya domin karrama wasu daga cikin zaratan ‘yan siyasar jihar Katsina ciki harda Dakta Mustapha Inuwa.

Daraktan yaɗa labaran yana magana ne a madadin sakataren gwamnatin jihar Katsina, inda ya ce duk wanda ke son zama da SGS dole ya kiyaye abubuwa guda biyu, idan kuma ba haka ba, ba zai taɓa zama abokin siyasar Mustapha Inuwa ba.

“A bi na farko shi ne, duk wanda yasan Mustapha Inuwa ya san shi a matsayin mutum wanda baya san ka je ka yi karya da shi, ko ka faɗi wani abun da bai yi ba, ka ce shi ya yi domin jama’a su so shi, Dakta baya san wannan” inji shi.

Haka kuma ya cigaba da bayanin cewa sharaɗi ba biyu shi ne, don kana son Mustapha ko kana tare da shi, baya son ka ci mutuncin wani a siyasa ko ka yi wa wani sharri don a guje shi a so Mustapha, ya ce duk mai wannan ba abokin tafiyar SGS ba ne kuma baya cikin tafiyarsa.

Alhaji Abdullahi Aliyu Yar’adua ya fito ƙarara ya bayyana cewa ita siyasar Mustapha Inuwa ba siyasa ba ce ta a mutu ko ayi rai ba, a a yana yi saboda jama’a suna ganin cancanta da kuma dacewarsa wanda har ya kai suke yi masa fatan alheri.

“Kuma idan jama’a ba su manta ba Dakta Mustapha Inuwa ya sha faɗa cewa idan shi ne alheri ga jihar Katsina da mutanen Katsina Allah da ke bada mulki ya bashi sannan ya ba shi ikon yin abinda ya kamata domin sauke nauyin al’umma” inji shi.

Sannan Yar’adua ya ƙara da ce Mustapha Inuwa ya fa da bakinsa sau tari cewa idan akwai wanda zai fi zama alheri ga jihar Katsina da mutanen Katsina to Allah ya kawo shi.

Ya ce wannan kaɗai ya isa mutum ya ƙara sanin wanene Dakta Mustapha Inuwa a siyasa, kafin a shiga ɓangaren irin gudunmawar da ya bada a siyasa, tun a manufa kawai ya banbanta da sauran ‘yan takara.

Daraktan yaɗa labaran ya ƙarƙare da cewa babu lokacin da za a yi magana akan wanene Mustapha Inuwa da irin gudunmawar da ya bada a siyasa musamman wuraren da ya yi aiki kafin zamansa sakataran gwamnatin jihar Katsina.

Tun da farko da yake nasa jawabin maraba ya yin gudanar da taro, shugaban kungiyar KDF Alhaji Gambo Agaji ya fara da godiya ga Allah tare da bayyana makasudin su na gudanar da taron Inda ya bayyana cewa sun shirya wannan taro ne domin kara sada zumunci, da kuma kara bayyana manufofin kungiyar da Kuma karrama wasu daga cikin muhimman mutane a jihar katsina.

Daga karshe ya yi addu’ar fatan alheri ga Dakta Mustapha Muhammad Inuwa akan kiraye kirayen da suke yi masa na ya fito takarar gwamnan jihar Katsina a shekara ta 2023.

Daga cikin wadanda aka karrama ya yin gudanar da taron, sun hada da sakataren gwamnatin jihar katsina Dakta Mustapha Muhammad Inuwa, da shugaban kungiyar K34 Dakta Abubakar Tsanni da dai sauransu.

Taron ya samu halartar shugabannin kungiyoyi iri daban-daban masu kira ga Dakta Mustapha ya fito takara 2023, shugabannin kungiyar na kananan hukumoni talatin da hudu da ke a jihar katsina, ‘yan siyasa maza da mata da sauransu

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *