2023: Idan APC Bata Tsaida Bola Tinubu Ba, Faduwa Zabe Za a yi -Sanata Abu Ibrahim
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Sanata Abu Ibrahim daya ne daga cikin aminai kuma shakike na Asiwaju Bola Ahmad Tinubu a wannan tafiya ta neman shugabacin kasa a 2023, ya bayyana cewa idan har jamiyyarsu ta APC ta yi kuskuren kin tsayar da Bola a matsayin dan takara to babu shaka fadauwa zabe za a yi.
Tsohon Sanatan yana magana ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayyan kammala ziyara da suka kawo a jihar Katsina ta sharar fage akan dan takararsu na shugaban kasa a zabe mai zuwa Bola Ahmad Tinubu
Duk wanda kasan ya zabi shugaba Buhari yana kaunar Bola Tinubu saboda haka idan har ka ce ba shi zaka zaba na a zabe mai zuwa, to babu abinda zai hana jam’iyyar APC faduwa zabe inji shi.
Sanata Abu Ibrahim ya bada amsa dangane da tirka-tirkar da ake yi akan batun yawan shekarun Bola tunibu, inda ya ce akwai shuwagabanin kasa a duniya da suka fi shi shekaru saboda haka wannan ba zai taba zama wani dalilin na kin tsayawa takarar Bola Tunibu ba.
Dangane da batun fitowar mataimakin shugaban kasa Ferfesa Yemi Osinbajo kuwa, Sanatan cewa ya yi basa tsoron fitowarsa takara, saboda yana da ‘yan cin yi haka, amma dai ya sani basa jin tsoronsa, kuma shi dan gidan Tunibu ne, Tinubu ya sama masa aiki, shi ya bada sunansa a matsayin da yake akai, ya ce inda kunya, ba ya ce zai yi gasa da ubangidansa ba.
Sama da mutun miliyan shan biyu da suka zabi Buhari suna ganin irin taimakon da Bola ya yi wa Buhari ya ci zabe, saboda haka suna san shi so sai, saboda haka idan aka ce ba za a tsaida Tunibu ba akwai mutane da yawa da ba za su fito kada kuria ba, sannan ina ganin abinda zai kawowa APC sauki shi ne ta ba Tinubu takara kawai inji shi Sanata Abu Ibrahim
Haka kuma Sanata Abu Ibrahim ya maida martani ga masu kalubalantar lafiyar Tinubu inda ya ce lafiyarsa lau, ya samu rauni a kafa, an yi masa aiki ya warke saboda haka babu wata matsala tare da shi a yanzu
