MATASHIYA ZUWA GA DUK AL’UMAR JIHAR KATSINA.
Alh. Dahiru Bara’u Mangal, Jigo a Nigeria kuma babban dan kasuwa kuma rikakken dan siyasa a jihar Katsina.
Nayi mamaki Matuka dana samu labarin Alh Dahiru Bara’u mangal ya bada makodan kudi har naira Billayan daya (1 billion) tallafi domin cigaban ilimin jihar Yobe.
A daidai lokacin da Jihar Katsina take daya daga jikin jahohi da suke koma baya wajen lalacewar ilimi, musamman ilimi na Primary dana Secondary.
Sai inga biliyan daya fa ba kananan kudi bane, dukda nashine kuma hakkinsane kuma dai-dai karfin sa munsan yana taimakawa amma sai inga “da arziki garin wasu gara garin ku” zaifi dacewa ace wanan tallafi jihar Katsia aka bawa shi kafin akaima wasu. da wanan biliyan dayar kawai na tabbatar za’a iya kawo gyara musamman ga makarantunmu na Primary dana secondary ba kadan ba. Sai inga indai gudummuwa akeso a bayar toh jihar Katsina tafi bukatar hakan. dubada yanayin da muke ciki. Ga talauci ga kuma tsadar rayuwa ga lalacewar ilimi, yayinda wasu makarantun ma a jihar basu zannuwa saboda karancin zaman lafia da rashin tsaro.
ina kira ga wannan Attajiri idan Allah ya mai dawowa gida Jihar Katsina lafia, ya kamata suma jihar Katsina yayi wani tsari dazai bada gudummuwa ta musamman domin ci gaban ilimin jihar da bamuda kamarta a Nigeria wato Jihar Katsina.
Allah ya kara kare jiharmu, sanan Allah ya kawo mana dauki na gaggawa halinda Jihar take ciki.
Haza bissalam
Yasir Ibrahim
Dan-Gwagwarmaya.
Dan Jihar Katsina.
