September 17, 2026

Sai Yanzu Ne Ake Kokarin Samar da canji a siyasar Jihar Katsina

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina.

Bisa dukkanin alamu jam’iyyar APC da kuma jam’iyyar PDP a jihar Katsina sun fuskanci samar da canji mai ma’ana a wannan zabe da ke tafe na kananan hukumomi da zai gudana nan da wata daya maii zuwa.

Tun daga yadda jam’iyyun ke fafutukar tsayar da ‘yan takara a matakin kansiloli da kuma shuwagabanin Kananan Hukumomi ya isa misalin cewa lallai akwai gagarumin canji duba da yadda aka rika yi a gwamnatocin baya.

Haka kuma hatta wadanda suka nuna sha’awar tsayawa takarar a matakai guda biyu ya nuna cewa lallai tsaffin kuraye sun matsa sun baiwa sabbin jini wuri domin su nuna ta su basira da kuma kwarewa.

Babu shakka dukkanin jam’iyyun sun nuna halin dattaku tun daga lokacin da aka ambata cewa za a gudanar da zaban Kananan Hukumomi domin cika alwarin da gwamna Aminu Bello Masari ya Yi tun kafin shigowarsa akan karagar mulki.

Kazalika sai a wannan lokacin ne babar jam’iyyar adawa ta samu kwarin gwaiwar shiga wannan zabe wanda zai kasance zakaran hwajin dafi akan zaban 2023 mai zuwa.

Yadda matasa suka yunkuro domin neman shugabancin a matakai daban-daban na kara nuni da cewa yanzu lokacin siyasar matasa ce kuma sun amsa kira domin suma a da ma da su yadda ya kamata.

Babar abin sha’awa shi ne hatta zaban fidda gwani da yake cikin gudana a ya yin da aka kammala mafiyancinsu, ya nuna cewa jama’a suna son a yi wannan zabe kuma sun shirya saboda haka abubuwa suke tafiya bisa tsari da lumana da kuma kwanciyar hankali.

Ya zuwa yanzu dai babu wani rahoto da ke nuna cewa an samu gagarumar matsala wajan gudanar da zaban fidda gwani, sai dai ‘ Yan matsaloli Nan da can.

Matasa wannan lokacin su ne, kuma dama ta samu gareki a karon farko a jihar Katsina, saboda haka dole ku yi amfani da ita saboda gaba.

Fuskokin da za su bayyana idan aka kammala wanann zabe za su kasance abin ban sha’awa a bangaran jam’iyyun guda biyu da wasu kuma idan an samu, saboda ina mai tabbatar da cewa lallai an samu canji daga bangaran matasa sun samu damar da za su dama a siyasa.

Ta bangaran gwamantin jihar Katsina kuwa sai dai a yaba mata saboda cika alkawari da gwamna Aminu Bello Masari ya yi na cewa zai tabbatar ya gudanar da zabe kafin karshen wa’adin mulkinsa, ga alama haka zata faru da yardar ALLAH.

Suma jami’an tsaro suna da gagarumin aiki a gabansu musamman tabbatar da cewa an yi wannan zabe an kammala lafiya ba tare da wata hatsaniya ba, idan suka yi haka sun sauke nauyin da ya rataya akan su na samar da tsaro a kowa irin yanayi.

Kananan Hukumomin da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga na daga cikin kalubalan da hukumomin tsaro za su maida hankali akan su domin ganin ma’aikatan zabe da masu kada kuri’a ba su fuskanci wata barazana ba daga ‘yan ta’ada ba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *