September 17, 2026

‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki a Wani Kauye mai Suna ‘Yar Malamai A Katsina.

0

Barayi da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kaii hari a wani kauye maii suna ‘yar Malamai da ke cikin karamar hukumar Kankara da ke jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa sun dauke mata da dama da suke akan hanyaarsu ta zuwa ‘yar malamai daga garin Makera duk a cikin karamar hukumar Kankara.

Wani da harin ya rutsa da kanwarsa mai suna Saifullahi Mato ya bayyana a shafinsa na fesbok cewa an dauke kanwarsa mai suna Fadila M Mato tare da wasu mata da ba a san yawan su ba.

Haka kuma Saifullahi Mato yana rokon addu’o’i domin samun sasarar kubutar wadanda aka dauka.

Wannan yanki dai na cigaba da fuskartar hare-haren’yan bindiga tare sace jama’a domin neman kudin fansa, lamarin da yanzu yana neman maida hannun ago baya aka. matsalar tsaro a jihar Katsina.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *