Matar Gwamnan Masari ga Matasa: Ku Kauracewa Miyagun Kwayoyi Ku zauna Lafiya
Daga Awwal Isah
Uwar gidan gwamnan jihar Katsina ta yi kira ga al’umomin ƙaramar hukumar Musawa da na Katsina da su ƙaurace ma ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Hajiya Hadiza Bello Masari ta yi wannan kiran ne a lokacin ƙaddamar da wata cibiyar gyaran hali da wata ƙungiyar da ba ta gwamnati ba haɗin gwiwa da Talban Musawa Abdullahi Aliyu suka kafa don bunƙasa rayuwar yara da mata.
Ta yi kira ga mutane da su yi amfani da cibiyar duba da cewa za ta gyara rayuwar mutanen da ke shan miyagun kwayoyi, tare da basu shawarar yadda za su guje ma hakan.
Tunda farko, saida babban jojin jihar Katsina mai shara’a Musa Ɗanladi Abubakar ya bayyana cewa, an kafa cibiyar ne da nufin bada shawara, tare da gyara rayuwar masu shan miyagun kwayoyi a yankin.
Kamar yadda ya ce, za ta taimaka wurin gyara rayuwar mutanen da suka yi nisa cikin shan miyagun kwayoyi.
Da ya ke magana a wurin, kwamishinan lafiya na jahar Katsina Engineer Yukubu Nuhu Danja, ya buƙaci mutanen yankin da su yi kyakkyawan amfani da cibiyar duba da mahimmancin ta, inda ya ce haɗarin shan miyagun kwayoyi na iya haifar da aikata laifuka a cikin alumma.
Shima da yake magana, hakimin Musawa Sagir Abdullahi Inde ya gode ma uwar gidan gwamnan da Talban Musawa Alhaji Abdullahi Aliyu kan wannan ƙoƙari.
