September 18, 2026

An gudanar da wani taron lakca na tunawa da Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakwato a Katsina

0

.

Daga Awwal Isah

Wata gidauniya ce mai suna Muryar Talaka haɗin gwiwa da wata ƙungiya mai suna “Save Katsina Group” suka shirya taron lakcar mai taken “salon shugabancin da ake buƙata”.

Taron lakcar na tunawa da marigayin dai, ta jawo hankalin shuwagabanni na yanzu da cewa suyi koyi da irin salon shugabancin da marigayi Sardaunan Sokoto ya yi.

A lokacin da uban taron ke magana, Kanwan Katsina hakimin Ƙetare Alhaji Usman Bello Ƙanƙara, ya ce salon shugabancin marigayi Sardaunan Sakwato ya zo da canje canje na alkairi a yankin arewacin Najeriya.

Kamar yadda ya bayyana, jami’ar ABU Zaria wadda marigayin ya kafa ita ce kan gaba wurin yaye mutanen da suka shugabanci Najeriya.

Shima shugaban taron da yake magana, mai shara’a Musa Ɗanladi Abubakar ya yi nuni da cewa ɓangaren shara’a ma ya amafana da irin kyakkyawan shugabanci na marigayi Sardaunan Sakwato wanda ya inganta arewacin Najeriya.

Mai shara’a Musa Ɗanladi Abubakar wanda ya samu wakilcin mai shari’a Ibrahim Isyaku Mashi, ya bayyana cewa marigayi Sardauna ya bunƙasa arewacin Najeria.

Tunda farko, saida shugaban kwamitin shirya taron Comrade Bishir Dauda Sabuwar Unguwa ya bayyana cewa, an shirya taron ne da nufin tunawa da marigayi Sardaunan Sakwato don amfanin aumma.

Taron lakcar wanda ƴan siyasa, da ɗalibai, da mata suka halarta, an shirya shi ne da nufin lalubo ma jihar Katsina dama yankin arewacin Najariya mafita.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *