September 17, 2026

Gwamnatin Katsina Hadin Gwiwa Da Kasashen Waje Za su Samar Da Jari Ga ‘Yan Kasuwar Katsina -Jikamshi

0

Daga Awwal Isah

Shugaban bunƙasa saka hannayen jari ta jahar Katsina, Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi ta sake nanata ƙoƙarin ta na samar da damarmaki ga masu zuba jari a jihar Katsina.

Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi ya bayyana hakan a lokacin da ya ke zantawa da ƴan jarida a Katsina dangane da kokarin da gwamnati ke wajan ganin an samu karin masu zuba hannun jari daga cikin gida da kuma ‘yan kasuwa daga waje.

Kamar yadda ya bayyana, gwamnatin jhar Katsina na yin haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ƙasashen waje, da ma’aikatar makamashi ta gwamnatin tarayya, dama sauran hukumomin da abin ya shafa don ganin an taimaka ma masu zuba jari na cikin ƙasa dama na ƙasashen waje.

Ibrahim Tukur Jikamshi ya kuma ce hukumar ta kammala tsare tsare da wata hukumar Nigeria mai bunƙasa fitar da kayayyakin cikin gida zuwa ƙasashen don kafa wata cibiya a kan hanyar Jibia, da za ta ƙunshi babban wurin aje kaya, da manya shagunan zamani watau super market”, da wurin parking na manyan motoci, da gidan mai, dama ofisoshi na jami’an tsaron dake kula da kan iyakokin Najeriya

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *