A Dauki Matakin Shari’a Kan Gwamnan Jihar Binuwai Samuel Ortom
Ra’ayin Mu’azu Hardawa Bauchi
Gwamnan Benue Samuel Ortom ya bukaci gwamnati ta ayyana dukkan kungiyoyin fulani irin su miyetti Allah a matsayin yan ta’adda kamar yadda aka ayyana kungiyoyin su Bello Turje, wato a maida dukkan fulani a Najeriya ‘yan ta’adda.
A lokacin da gwamnonin Taraba da Binuwai suka bukaci fulani su fita daga jihohin su da dabbobinsu sun haramta kiwo Kuma idan za su fita saiko su nemo tirela su kwashe shanun su zuwa jihohin arewa.
Lokacin wannan furuci mun yi ta rubuce rubuce cewa shugaban kasa ya kirasu ya ja kunnen su idan ba haka ba sun hura wutar da ba a san ranar mutuwarta ba, haka aka barsu har aka yi ta kashe fulani da dabbobin su a yankin Sarsauna Mambilla.
Da haka aka fara kashe fulani ana kwashe dabbobinsu idan sunje ofishin masu tsaro ko yan banga ayi ta karbar kudi alhali dabbobi sun jima da isa kudanci.
Da haka aka maida fulani saniyar tatsa rana zafi inuwa kuna daga bisani suka zama ‘yan bindiga aka shiga halin da ake ciki yanzu kuma Ortom na Benue na neman kara hura wutar gaba da neman daukar fansa don haka yadda za su nemi ayyana a basu kasar ‘middle belt’ kamar yadda ‘yan Biafra ke yi, shine next level.
Ya kamata gwamnatin tarayya ta dauki mataki tun kafin Najeriya bata sake shiga wani mummunan sabon ‘extra level’ ba. Allah ya kawo mafita.
