September 17, 2026

Yadda CDP Suka Hannanta Takin Zamani Ga Manoma a Fadin Jihar Katsina

1779192608828

 

Yanzu haka shirin bunƙasa rayuwar al’umma a jihar Katsina wato community Development Program (DCP) na cigaba da hannanta takin zamani ga manoma a fadin jihar Katsina

Takin wanda gwamnati ta bada umarnin a sayar da shi akan farashi mai rahusa kowane buhu naira dubu ashirin da biyar ya sauka hannun manoma.

Tsarin tafiyar da wannan shiri na karkashin kulawar Dakta Kamaluddeen Kabir inda ake wannan aiki a gundumar Makera Dikke da kuma Mai Ruwa da ke ƙaramar hukumar Funtua a jihar Katsina

Sannan akwai wakilan wannan shiri a mazabo 361 domin su tabbatar da adalci ga waɗanda suka biya kuɗin su lakadan domin tunkara daminar bana da ke tafe

Kuma gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa ta ɗauki nauyin kai takin zamani lungu da sakon da za a raba shi ba tare da manomi ya biya ko sisi ba na ɗaukar kaya.

About The Author