Kwana 100 Na Shuwagabannin Ƙananan hukumomin Katsina, Shin Ko ƙaramar hukumar Mashi Tasan Ana yi?
Daga Jamilu Sama’ila Ɗanɗana
Shuagabancin ƙananan hukumomi a jihar Katsina, ya shafe fiyeda kwana ɗari da somawa, Saidai babu wani ciagaba face; Irin ciagabn mai ginan rijiya a karamar hukumar Mashi, domin har ɗarin ta ɗora, amma ba’a ɗora aniyar yin komai ba.
Shifa shuagabancin karamar hukuma, anyi sane Domin kusanta gwamnati ta zama kusa da talaka, domin ya samu sauƙi Wajen gabatar da buƙatu da matsalolisa yadda za’a Magance masa! Amma mu a karamar hukumar mashi, gwara Kujerar ta zama babu kowa, da halin da take ciki a yanzu.
Munada tarin Matsaloli, wanda Kuma haƙkin shugaban karamar hukuma ne, ya magancesu, amma inbanda tarin posting babu abinda akayi.. wanda hakan manuniyace dake nuna babu abinda za’ayi.
Yakamata (Honorable) Ciyaman yasani: Karamar hukumar mashi, tsayuwa takeso ayi bisa matsalolinta, ba tsayawa ayi hoto a ɗora a saman facebook ba, domin tuni mun wuce wannan shafin. Anyi kwana 100 babu komai, munaso ayi wani abu domin anfanuwar al’umma.
