September 19, 2026

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Shida A Kauyen Plateau.

0

Akalla mutane shida ne aka ruwaito cewa an kashe ranar Talata lokacin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari kauyen Pinau dake karamar hukumar Wase ta jihar Plateau.

An bada rohoton cewa barayin sun lalata kadarori da barasa tare da kayan abinci da sauran kayayyaki masu daraja na al’umma.

Mai magana da yawun rundunar ‘Operation Safe Haven (OPSH)’ da ke aiki da jami’an tsaro da dama mai kula da zaman lafiya a Plateau, Manjo Ishaku Takwa ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce an tura sojoji zuwa wurin da lamarin ya faru.

Wani mazaunin unguwar da ya yi magana ta wayar tarho ya ce ‘yan bindigar sun isa unguwar ne da misalin karfe 3:00 na rana, inda aka harbe mutane shida tare da jikkata wasu da dama.

An bayyana cewa kashe-kashen na zuwa ne kwanaki biyar bayan da mazauna unguwar suka bayyana fargabar su kan janye sojoji daga yankin, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Sunnews.

Lamarin dai ya tilastawa daruruwan mutane da suka hada da mata da kananan yara tserewa daga cikin al’ummar saboda fargabar kai hari a hedikwatar karamar hukumar Wase.

Wani mazaunin garin Garba Kasuwa da ya arce daga gidansa ya bayyana cewa maharan sun zo ne kan babura dauke da manyan bindigogi.

Ya ce “Kafin zuwan ‘yan ta’addan, tuni daruruwan mazauna unguwar suka gudu saboda tsoron kada a kai musu hari, shi ya sa adadin wadanda suka mutu bai yi yawa ba. Kadan da suka rage, an kashe wasu. ‘Yan fashin da isowarsu suka bukaci mutane da su rufe kansu a dakunansu.

Ya ce, “Sun fasa shagunanmu sun sace kayan abinci da sauran kadarori. Sun kuma yi garkuwa da wasu mutane”.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *