September 17, 2026

Kungiyar Katsina United Za Ta Ba Yan Wasan Gida Damar Gwada Bajintarsu.

0

A kokarinta na fadada wa tare da bunkasa sabuwar kungiyar kwallon kafar Katsina United, hukumar gudanarwar kungiyar ta amince da gayyatar wasu zababbun yan wasa yan asalin jihar wadanda suka tsallake matakai daban daban domin halarta tantancewa ta matakin jaha.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na kungiyar Nasir sani Gide ya fitar kuma aka raba ma manema labarai.

Sanarwar ta ambato shugaban kungiyar prince Abdussamadu Badamasi ya na bayyana cewa masu horar da kungiyar ne za su tantance waɗanda aka zabo ɗin a lokacin aikin horaswar na gwaji, inda za a zaɓi waɗanda suka fi kwazo a karshen atisayen gwajin.

Prince Abdussamadu Badamasi ya bayyana cewa za a tura takardar gayyatar zuwa ga kungiyoyi daban na shiyyoyin jiha ukku, inda ya tabbatar da cewa za a yi ma yan wasan da suka chanchanta rijista da kungiyar ta Katsina United.

Ya Kara da cewa, za a basu lokacin wasa sosai a yayin kakar wasa mai zuwa.

Yayi nuni da cewa, matakin nada nufin baiwa yan wasan gida dama, tare kuma da bunkasa kungiyar.

Daga karshe dai sanarwar ta bukaci yan wasan yan asalin jihar da su yi amfani da damar da aka basu domin jihar ta cimma kudirinta na bunƙasa bangaren wasanni.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *