September 18, 2026

Gwamnan Jihar Cross River Ya Yi Taren Yan Makara A Gidan Gwamnatin Jihar.

0

A safiyar yau Laraba ne gwamnan jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade ya kulle ma’aikatan gwamnati da ke aiki a gidan gwamnati da ke Calabar saboda sun makara wajen aiki.

Majiyar Popular News Hausa ta Vanguard ta bada rohoton cewa, gwamna Ayade wanda ya zo aiki kafin karfe 8:00 na safe ya umurci babban jami’in tsaro, da ya kulle kofar ofishin gwamnan kuma kada abari wani ya shigo bayan karfe 8:00 na safe.

Majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard ta ce wakilinta ya samu ma’aikatan gwamnati kimanin 100 bakin kofar shiga gidan gwamnatin a lokacin da ya ziyarci ofishin gwamnan da misalin karfe 10:45 na safe, bayan ma wadanda suka fice.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa jaridar cewa, gwamnan ya yi mamakin ganin da yawa daga cikin ma’aikatan ba su shiga ofis ba a lokacin da ya zo.

“Nan da nan ya ba da umarnin a dawo da littafin daukar sunaye, sannan ya umarci babban jami’in tsaro da ya kulle kofa saboda kada wanda suka makara su shigo, in ji majiyar.

Bincike ya nuna cewa wadanda aka taren sun hada da ma’aikata daban-daban, ciki har da babban jami’in ma’aikatan gwamnatin jihar da kuma wadanda aka nada a siyasance ciki har da masu ba da shawara na musamman.

Da aka tuntubi mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Mr. Christian Ita, ya ce a ko da yaushe gwamnan ba ya son rashin da’a sannan kuma yana bada tukuici ga wadanda suka jajirce wajen gudanar da ayyukansu.

Kalamansa: “Lokacin zuwa wurin aiki shi ne karfe 8 na safe kuma idan gwamna zai iya kasancewa a ofis a lokacin, me yasa wasu ba za su iya kasancewa a wurin ba.

“Gwamna a ko da yaushe yana bada tukuici, kuma ba ya shakkar hukunta masu laifi, idan sun saɓa doka. Ya na kuma bada kyauta lokacin da ma’aikata suka himmatu wajen yin aiki,” inji shi.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ana ganin ma’aikata da dama tsaye bakin kofar shiga gidan gwamnatin jihar, yayin da wasu kuma suka koma kan harkokin masarautunsu.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *