November 18, 2026

Kungiyar Izala Ta Nada Abdulhadi Bawa Cikin Kwamitin Kula Da Masu Lalurar Ciwon Ido A Katsina

0

Kungiyar Izala ta nada AbdulHadi Ahmad Bawa cikin kwamitin kula da masu lalurar ciwon ido, sakamakon rasuwar shugaban kwamitin Malam Ahmad Bawa Faskari

A Ranar Lahadin da ta gabata ne Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah na Jihar Katsina, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah) ya tabbatar da nadin Alhaji Ibrahim Dabo Bujawa a matsayin sabon Shugaban Kwamitin kula da masu lalurar ido na Jihar Katsina a karkashin wannan Kungiya tare da za6ar Alh. Abdulhadi Ahmad Bawa Faskari cikin wannan Kwamiti

Wannan nadin ya biyo bayan rasuwar Shugaban Kwamitin Alhaji Ahmad Bawa Faskari wanda ya kasance Shugaban Kwamitin tun shekarar 1998 zuwa ranar da Allah yayi ma rasuwa 18 February, 2022

A tsawon lokacin da aka dauka yana jagorantar wannan Kwamiti Dubbannan mutane ne suka amfana da: Aikin Ido, Magani da Gilashi kyauta

Muna rokon Allah ya ba su ikon sauke wannan nauyi da aka daura masu. Ya kuma gafarta ma tsohon Shugaban ya karbi ayyukan shi na alkhairi ya gafarta ma shi kura kurensa

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *