Zaɓan 2023: Nazari Akan Wasu Kalaman Dakta Mustapha Muhammad Inuwa (1)
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina.
Batun takarar Mustapha Muhammad Inuwa bai zama bako ba, domin kuwa duk wanda ya kwana ya tashi a Katsina ya san da wannan maganar kuma yana jiran lokacin wannan takara.
Sai dai wani al’amari da zama bako ga jama’a shi ne yadda Mustapha ya fito fili ƙarara cewa tunda ake wannan batu na takarar gwamnansa mai taɓa yin magana da wani ko wasu ba cewa zai tsaya takara a zaɓen 2023.
Dakta Mustapha Inuwa ya ce idan akwai wani mutum da na taɓa gaya masa zan yi takara ya fito ya bayyana saboda yana ganin akwai aikin da ya kamata su maida hankali akan sa ba wai maganar takara ba da lokaci bai yi ba.
A lokacin ayyana wannan batu na takarar gwamna Dakta Mustapha Inuwa ya yi wasu maganganu basu tada hankali wanda ya da ce ace kowane ɗan siyasa ya yi nazarin su ya kuma yi karatun ta nutsu akan hikimar siyasar da ke ciki.
Tunda farko sai dai Dakta Mustapha Inuwa ya ziyarci ofishin jam’iyyar APC na jihar Katsina domin sanar da su wanann kudiri na shi, daga bisani kuma ya tara manema labarai ya saboda duniya wanann aniya ta sa.
Ba wannan ne baban muhimmin abu ba, maganganun da ya yi a wadanda wurare guda biyu, na tabbatar da mai karatu idan zai nutsu ya karanta ya ɗora wanann batu akan ma’auni na hankali da tunani babu shakka zai amfana a siyasa da zamantakewar rayuwa.
Bayan kammala jawabin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Alhaji Sani Aliyu (JB) wanda ya yi lale marhabin da zuwan wannan ɗan takara da ya bayyana a matsayin bana bako wanda shi kaɗai ɗan takara da jam’iyya ta sani.
“Ya zuwa yanzu duk wadannan suka nuna sha’awar yin takarar gwamnan jihar Katsina, Dakta Mustapha Inuwa ne kaɗai ya zo nan gaban jam’iyya ya sanar da ita, saboda muna yi mashi fatan alheri” inji JB.
A jawabin da Mustapha Inuwa ya yi a ofishin jam’iyyar APC ya ce bayyana cewa wannan takara da ya fito ba ya fito ba ne akan a mutu ko ayi rai ba, ya ce yana don ayi bi tsari da zai kai ga ba jam’iyyar APC nasara a zaɓe mai zuwa.
Sannan ya kara da cewa kafin ya yanke shawarar tsayawa takara, sai da ya fara zama ya tattauna tare da mai gidansa, (Gwamna Aminu Bello Masari) suka fahimci juna bayan ya gaya masa buƙatar sa ta neman kujerar gwamnan jihar Katsina, ya kuma ba shi ƙarin gwiwa.
Ya cigaba da cewa, bayan wancan zama abu na gaba da ya yi shi ne ya zo ofishin jam’iyyar APC domin ya sanar da wannan aniya ta sa, kuma gashi ya zo ya samar da ita kamar yadda tsari ya tanada, jam’iyya ita ce gaba domin kuwa yana ƙarƙashinta.
“Idan muka koma ko ga Addini da al’adar Malam Bahaushe, duk lokacin da wani ya ga wata budurwa ya ji yana son ta, abinda aka sani shi ne zai nemi izni daga manya, idan an bashi sai ya nemi yarinya su daidai ta, to uwar jam’iyya Mustapha Inuwa na ga ɗiyar ku ina so a bani izni in nema.” In ji Mustapha Inuwa.
Mustapha Muhammad Inuwa ya ƙara da cewa idan zaman gwamnan jihar Katsina zai zama alheri ta jihar da kuma mutanen Katsina Allah ya bashi gwamnan jihar Katsina idan kuma akwai wanda zai zama alheri fiye da shi Allah ya kawo shi saboda jihar Katsinan ce a gabansa ba wai kan sa ba
Kazalika Mustapha ya yi bayanin cewa duk wata hidima da ake gani wanda ta shafi wanda takara tasa da suka haɗa da buga fostoci da wakoki da rubuce-rubuce a kafar sadarwa ta zamani, babu wani mutum da Mustapha ya ce ya yi ko ya bada kuɗi ya ce ayi.
Ya ce tun kafin a rantsar da gwamna Aminu Bello Masari a karo na biyu wasu suka fara wanan kiraye-kiraye domin ta fito ya tsaya takarar gwamnan jihar Katsina, amma sai yanzu ya amsa wannan kira na su.
Zamu cigaba insha’Allahu…
