Zaman Lafiya Shine Abinda Ke Kawo Cigaba Ga Al’umma- Kungiyar Wanda Da Zaman Lafiya
Daga Babangida Sunusi, Kano
Aranar talatane kungiyar wanzar da zaman lafiya da kawo sasanci da sulhu tsakanin mutane ta jahar Kano hadin gwuiwa da Kungiyar gamayyar Turawa bisa jagoranci majalisar kasar bnirtaniya suka gudanar da taron bita ga membobinsu yadda dazasu shiga lungu da sako dan wayarma da al’umma kai gameda amfanin zaman lafiya da sulhu a tsakanin juna.
Kungiyar da MR Adeniyi Aremu ke jagoranta anan Kano ta gudanar da taron na rana dayane adakin taro na Tahir Guests Palace inda ta gayyato jama’a daban daban tun daga kan jagoranci malaman Addinai na islama da bangaren coci-coci tare da shugabanin qungiyoyin kare hakkin al’umma da jami’an gwamnati hadi da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
Dayake jawabi ga manema labarai shugaban tafiya Mr Adeniyi Aremu yace lallai wannan hanyarne yadace subi wajen wayarma da masu ruwa da tsaki kai dan suma suje tareda tara jama’ar su dan isar da wannan sako.
Mr Adeniyi Aremu yakuma ƙara dacewa aikinsune ayanzu wajen sa ido tare da hada hannu da jami’an tsaro wajen yaƙar bangar siyasa magance shaye shaye daidaito da sulhunta al’umma wanda yana daya daga cikin abinda yasa suka nemi Mai girma Kwamishinan Yan sandan jihar Kano CP Sama’ila Shu’aibu Dikko yabasu layukan wayar kaf DPO’s dake kula da ofisoshin shiya na kananan hukumomin dake Kano dan aiki tare wajen kawar da mugayen dabi’u da magance matsalolin yau da kullum.
Shima Prof Muhammad Bello Shitu na jami’ar Bayaro dake Kano daya gabatar da muƙala ko takarda yace sungayyaci al’ummane dan su bayyana hanyoyin dazasu iya kawo dauki da Kuma abubuwan dasuke rura wutar rashin zaman lafiya.
M B shitu yakuma kara dacewa wasu dayawan mahalarta taron sun bayyan cewa yawancin rashin fahimtar da matsalar na fitowane daga shugabanin Addinai da majami’u ne wajen rashin sanin yadda zasu wa’azantar ko Kuma isar da sakon dasuke san isarwa zuwa ga mabiyansu.
Professor Shitu yakumace sunja hankalin mahalarta taron yadda zasuyi wajen nunama magoya bayansu mahimmanci zaman lafiya da yadda zasu kaucewa kalaman ɓatanci dazai iya tunzura wasu har yakaiga tashin hankali dan su wayarma da mabiyansu kai tareda nuna masu illolin da abin ke haifarwa.
Shima malam Hadi Ibrahim dayake limamin masallacin juma’a na hotoro qaramar hukumar Tarauni ya nuna matukar jin dadinsa ga wannan taro, inda yace lallai Kano tana kan gaba wajen wanzar da zaman lafiya shiyasa mafi yawan taruka ana kawosu jahar Kano.
Yakumayi Alkawarin fadakarda jama’a lokacin sallar juma’a kan wannan taro dan nuna mahimmanci zaman lafiya tare da yadda shugabbaninsu suna kokarta nuna zaman lafiya atsakanin al’umma.
Hakama abayinta shugabar mata Yan jaridu ta jahar Kano Bilkisu Zango tace lallai angudanar da wannan taro kan gabar da ake buqatarsa.
Sannan takuma bukaci jama’a dasu ara kokarin wayar da kan jama’a da shugabaninsu amfanin zaman lafiya tsakanin Al’umma musamman yanzu da siyasa.
Sannan tace matasa jami’an tsaro da malamai sune kangaba wajen wayarma da jama’a kai kan rashin amfanin tashin hankali acikin Al’umma to yakamata kowa yayi matukar zaburarwa wajen koyarwa da wanzar dazaman lafiya.
