Kin Gudanar da zaɓen Fidda-Gwani a Mazaɓar Bede/Jakusko Karan-Tsaye Ne Ga Dokar Zaɓe – Jama’ar Yankin
Daga Sharafudeen Al-Amin, Yobe
Magoya bayan ‘yan takarar kujerar majalisar wakilai a jam’iyyar APC da ke mazaɓar Bade/Jakusko a jihar Yobe, suna ci gaba da guna-gunin rashin gudanar da zaɓen fidda-gwani a mazaɓar, sama da awanni 24 da fara zaɓen a sauran mazaɓu a jihar da ma ƙasa baki ɗaya, al’amarin da ke ci gaba da jawo tayar da jijiyoyin wuya tare da rashin sanin makomar siyasar yanki.
Ra’ayoyi da dama daga bakin jama’ar waɗannan ƙananan hukumomi guda biyu; Bade da Jakusko sun shaida wa wakikinmu ƙorafinsu tare da tambayar neman sanin dalilan da ya sa aka ƙi gudanar da zaɓen a Government Lodge da ke garin Gashuwa, wanda nan ne cibiyar aka saba gudanar dashi a yankin, kamar yadda dokar zaɓen ta tanada tare da sauran yankuna a faɗin ƙasar nan.
Haka kuma, tun kimanin qarfe 7:30 na safiyar ranar juma’a jama’a suke da ko, amma babu ko ɗaya daga jami’an kwamitin zaɓen jam’iyyar APC da aka turo daga Abuja ko na INEC da ya taka ƙafarsa a wajen a tsawon yinin.
Mohammed Suleiman ya na ɗaya daga cikin magoya bayan da ya bayyana rashin gamsuwarsu dangane da take-taken masu ruwa da tsaki a harkar zaɓen fidda-gwanin, alhalin an gudanar da zaɓen a sauran yankuna guda shidda (6) da ke jihar, saɓanin mazaɓar Bade/Jakusko, wanda har lokacin rubuta wannan rahoton (ranar Lahadi) ba a gudanar dashi ba.
“Sannan abin da ya ɗaure mana kai shi ne, yanzu haka ana gudanar da zaɓen fidda-gwani na sanatan yankin, amma uwar jam’iyyar APC taƙi tace uffan dangane da ƙin gudanar da na majalisar wakilai a wannan mazaɓa tamu.”
“Har wala yau, abin zargi ne idan dai har za a gudanar da zaɓen a yankin da yake fuskantar matsalar tsaro amma ayi kunnen uwar-shegu da na yankinmu.”
“Amma mun samu labarin wai an tura zaɓen zuwa Damaturu, fadar jihar Yobe, amma duk da hakan babu abin da aka gudanar a can ɗin ma.”
Mohammed ya yi zargin cewa bisa wasu ɓoyayyun bayanan da ake nuku-nuƙu da su sun nuna ana ƙoƙarin karkata akalar takarar ga wani shafaffe da mai, wanda wasu manya ke son a ba.
Premium Times Hausa ta tuntubi ‘yan takarar, domin jin ra’ayoyinsu, wanda Hon. Sani Ahmed Kaitafi ya bayyana cewa, sun yi duk shiri da tsarin da doka ta tanada kan zaɓen amma har yanzu basu san me yake faruwa ba, face sai rufa-rufa ake musu; ba a fito fili ƙarara ba wajen gaya musu dalilin da ya sa ba a gudanar da zaɓen ba.
Kaitafi ya ce, “Tun ranar juma’a da aka tsara gudanar da zaɓen muke jiran jami’an zaɓen, amma shuru, amma daga baya mun samu labarin an kwashe delegates din Bade da Jakusko zuwa Damaturu. Hakan yasa na kira jami’an zaɓen don su yi mana bayanin yaushe za a gudanar da zaɓen? Shi ne suka ce har sun kamo hanya, sun kusa Potiskum aka ce wai su dawo Damaturu, shi ne na ce wa ya ce ku dawo? Sai suka ce umurni ne daga sama.”
“Daga baya shima aka umurci shugaban ƙaramar hukumar Jakusko ya tafi Damaturu, wai can za a yi zaɓen. Amma nayi mamakin me ya hada Damaturu da zaɓen majalisar wakilai (House of Representative)? Alhalin dokar zaɓe ta ce a Gashua za a yi shi.
A haka na wuni a ranar juma’a, sai kimanin 8:00pm na fita zuwa Damaturu. Ina zuwa na tarar da Ya’u Galadima, Mohammed Karage da Madaki Manu Girgir a Presential Lodge, muka gaisa kuma na tambayi jami’an zaɓen cewa me ya sa ba a gudanar mana da zaɓe ba? Shi ne suka ce na bari za a yi magana, amma shuru babu cikakken bayani.”
“Amma da na binciki shugaban kwamitin zaɓen da aka turo daga Abuja, Mallam Umar Kareto, shi ne sai ya tabbatar min cewa nayi hakuri gobe (Asabar) za a zo haɗa na mazaɓar Bade/Jakusko da zaɓen sanatan Arewacin Yobe.”
“Shi ne muka sake dawowa Gashua, muka sake tattara delegates don su zama cikin shiri, tsammaninmu idan an gama na Sanatan za a yi na wakilai, amma shuru babu labari, sai daga baya muka samu kishin-kishin cewa wai an ba Ya’u Galadima takara a Damaturu, kuma wai sakataren jam’iyyar APC ya ce a tafi Damaturu da DSS, Police, jami’an INEC tare da party chairman na Bade da Jakusko.”
“Hakan ya sa muka zura musu idanu, kuma daga nan bamu san me yake faruwa ba, duk wanda muka kira sai ya ce bai san me yake faruwa ba. Sannan mun so ace sun fito fili sun shaida mana cewa ‘Kai Sani ba ma son ka yi takarar nan’.
Duk da akwai maganar da naji a wata majiya cewa an kirasu ne daga sama cewa kar a bani takara. Shi ne sai jami’an suka gaya wa shi wancan babban mutum cewa su bari ayi zaben, shi ne ya gaya musu cewa ai kowane zaɓe za a yi Sani ne zai ci, saboda haka kar ma ayi zaven.”
Wakilinmu ya nemi tambaye shi cewa wane mataki zai ɗauka idan abin ya ci gaba da kasancewa a haka? Shi ne sai ya ce, “Ai ɗaukar matakin ba nawa bane ni kadai, sai mun zauna da sauran yan takarar, saboda yanzu haka zancen da ake suna Damaturu.”
Ya ƙara da cewa, “Amma ta bangarena, yau zan kira uwar jam’iyyar APC don suyi mana cikakken bayani dangane da dalilan da suka saka ba a gudanar mana da zaɓen ba, saboda gashi lokacin zaɓen fidda-gwani ya wuce, daga nan sai na kama gabana.
Kuma ni da jama’ata zamu zauna wuri guda domin daukar matakin bai-daya, amma ni kadai ba zan ɗauki wani mataki ba zamu zauna mu san abin da zamu yi.”
A nashi ɓangaren, mun nemi jin ta bakin Hon. Zakari Ya’u Galadima ta hanyar wayar tafi-da-gidanka, a matsayinsa wanda shi ne Dan majalisa mai wakiltar yankin, kuma xaya daga cikin yan takarar, inda ya kada baki ya ce, ya na jiran abin da uwar jam’iyyar za ta ce kan lamarin, amma ba zai iya cewa komai ba kan al’amarin.
Shi kuma Mohammed Manu Girgir ɗaya dan takarar, ya nuna cewa babu wani zaɓen da aka gudanar a mazavar, wanda Fadar hakan ke da wuya ya katse kiran, wanda na sake kiransa amma yaƙi ya daga.
Har wala yau, duk ƙooarin jin ta bakin shugaban jam’iyyar APC a jihar Yobe, Muhammad Gadaka tare da Sakataren sa, Abubakar Bakabe abin ya faskara; babu xaga kira ballantana mayar da jawabin saqon kar-ta-kwana da na tura musu.
A hannu guda kuma, jami’in hulxa da jama’a na jam’iyyar APC a jihar Yobe, Bakura Jibrin ya ce zancen ya zarta mafidda-gwanin ya ce wani abu a kai.
