September 18, 2026

Yadda Sojoji Suka Riƙe Dukan Daliget Harda Matan Aure A Daura Domin A Kayar Da Ni Zaɓe -Hon. Fatuhu Ɗa Ga Buhari

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Mai’adua da Daura da kuma Sandamu Hon. Fatuhu Muhammad Ɗa Ga shugaba Buhari ya ce wasu marasa kishin Daura da shugaban kasar Muhammad Buhari sun yi amfani da karfi wajan kada shi zaɓen fidda gwani da aka yi jinya a Daura.

Ɗan Majalisar ya bayyana haka ne a garin Daura a lokacin da yake zantawa ta ‘yan jarida dangane da cin zarafin da ya ce anyi wa magoya bayan sa musamman matan aure da sojoji da ‘yan sanda suka rika duka haka kawai.

Sai dai Hon. Fatuhu Muhammad ya ce babu wanda ya kitsa wannan al’amari sai tsohon Kwamishinan Shari’a kuma mai baiwa uwar jam’iyya shawara akan harkokin Shari’a Barista Ahmad Usman El-Marzuq tare da wasu mutane da ya ce sai nan gaba sai faɗin sunayansu.

“Da mun yi niyyar ba zamu shiga wannan zaɓen ba, sai muka ga idan muka yi haka, jamiyyar APC na iya rasa ‘yan takara, amma duk da haka mun yi ƙoƙarin jawo hankalin uwar jam’iyya cewa ga wata fitina nan a gyara kafin ta iso, ba su ji ba.” In ji shi

Ya ce idan aka duba so sai, wannan mazaɓa da ya fito daga cikin ta ita ce mazaɓar shugaban kasar Muhammad Buhari sannan duk wannan abu da ake yi masa Ɗa yake ga shugaba Buhari domin ya ce da mahaifinsa da Buhari uwa ɗaya uba ɗaya suke.

Hon. Fatuhu ya ƙara da cewa baban abinda ya kawo wannan hargitsi shi ne, saboda kayan da ya yi wa tsohon Kwamishinan Shari’a Barista Ahmad El-Marzuq a zaɓen Daliget da aka yi a baya. Inda ya ce duk waɗanda ya tsaida takara suka samu nasara.

Ya ce a matsayin sa na wanda yasan doka da kuma la’akari da gidan da ya fito ya ce zai bi kadin wannan al’amari ta hanyar bin doka da oda, sai dai ya ce yana san ayi adalci amma idan ba a yi ba to sai nan gaba za su duba su ga matakin da za su ɗauka.

“Babu wanda ke haɗa wannan rigima sai tsohon Kwamishinan Shari’a Barista Ahmad Usman El-Marzuq kuma mai baiwa jam’iyyar APC ta ƙasa shawara saboda na kayar da shi zaɓe” Hon Fatuhu.

Ɗan Majalisar ya ce baban abinda ya ɓata masa rai a wannan hayaniya shi ne yadda aka turo sojoji suka riƙa dukan masu zaɓen fidda gwani (delegates) ci harda matan aure a ya yin da ‘yan sanda suke riƙe harba masu barkonon tsohuwa (tiagas)

“Akwai takaice a wannan lamari ace an canza sunayen masu zaɓen fidda gwani (delegates) halastace an maye gurbinsa da na bugi wanda tsohon Kwamishinan shari’a ya yi domin dai kawai a kayar da ni zaɓen fidda gwani.

Sannan kuma ya yi zargin cewa akwai waɗanda ke taimakawa Barista Ahmad El-Marzuq da kuɗi da jami’an tsaro daga Abuja wanda domin ƙara rura wutar rikicin, inda yasa ce idan aka tambaye El-Marzuq zai faɗi ko su wanene tunda ya san su.

Hon. Fatuhu Muhammad ya shaidawa jama’arsa da su kwantar da hankalinsu kadda wanda ya tada wata fitina za su bi kadin abinda ya faru a matakin shari’a kuma tuni aka fara bin hanyoyin da suka da ce.

Hon. Fatuhu Muhammad ya ce tuni suka rubuta kokensu ga kwamitin karbar korafi na wannan zaɓen fidda gwani da aka yi domin su ga abinda Uwar jam’iyar ta APC zata yi, ya ce idan ta yi adalci shikenan idan kuma bata yi ba, to za su zauna da shi magoya bayan sa domin ɗaukar mataki na gaba.

Haka kuma duk ƙoƙarin da muka yi domin ji daga bakin wanda ake zargi da zama kanwa uwar gami a wannan al’amari wato tsohon Kwamishinan shari’a kuma mai baiwa jam’iyyar APC shawara akan harkokin shari’a Barista Ahmad Usman El-Marzuq ya ce ba zai ce komi ba a yanzu.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *