September 18, 2026

APCON Ta Bayyana Shirinta Na Sanya Ka’ida Ga Tallace Tallacen Sadarwar Zamani A Najeriya.

0

Jaridar VANGUARD ta ce, Majalissar kula da tallace-tallace ta Najeriya wato APCON, ta kaddamar da tsare-tsare na daidaita tallace-tallace ta yanar gizo a kasar nan, a wani mataki na tsaftace masana’antar da kuma dakile sakonnin tallace-tallace masu tayar da hankali.

Shugaban hukumar Olalekan Fadolapo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wurimn wani taro da ya gudana a otal din Sheraton da ke Lagos a ranar Litinin.

Ya ce APCON za ta dauki mataki kan daidaikun mutane da kungiyoyin da ke yin talla ba tare da an ba su lasisi daga majalissar APCON ba.

Ya kara da cewa majalisar a shirye take ta tabbatar da bin ka’idojin talla ta yanar gizo daidai da tanade-tanaden kundin tsarin talla na Najeriya.

Don haka, ya bukaci kamfanoni, masu sana’ar sadarwa, da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa an tantance tallar su ta yanar gizo kafin gudanar da su.

Hakazalika, ya bukaci masu neman mukaman siyasa da su tabbatar da cewa an tantance tallace-tallacen su na siyasa kafin watsa su a kowace kafar sadarwa yayin da kakar zabe ta gabato.

Bugu da kari, Fadolapo ya bayyana cewa majalisar ta cika makil da korafe-korafe kan tallace-tallacen da ba su dace ba da ake watsa wa a kafafen yada labarai na yanar gizo da ke cin karensu babu babbaka a Najeriya.

Ya bada misali da wata talla da wani banki ya yi ta yanar gizo kwanan nan da ta jawo cece-ku-ce a kasar nan, wanda da yawa suka bayyana ta a matsayin abin takaici.

A cikin tallar dai, an kwatanta tashin “Yesu Almasihu” daga matacce da wani “Biredim Agege”.

Fadolapo ya bayyana cewa tallace-tallace da yawa dake yawo kan shafukan yanar gizo da shafukan sada zumunta sun sabama addinai da al’adun wasu mutanen kasar nan don haka sai APCON ta tantance su.

“Tare da karuwar ayyukan kafofin watsa labarai na dijital a Najeriya da samun damar hanyoyin sadarwa na yanar gizo, mun fuskanci sabuwar barazanar tallar da ba ta dace ba da tada hankali da kayayyakin sadarwar talla wadanda ke da duk wani yuwuwar rura wutar rikicin addini, lalata tarbiyya, da kuma bayanan da ba su dace ba yayin da an ba da izinin bunƙasa tare da mummunan tasiri ga ƙasar, tattalin arzikinta da tsarin darajarta.”

“Shigowar yanar gizo da sabbin kafafen sadarwa irin su Blogs, Facebook, Twitter, Instagram, WhatsApp, Google, Facebook, Twitter, YouTube, da dai sauransu ya kawo sauyi a harkar sadarwa a duniya, inda hakan ya sa suke sabama ka’idar Tallace-tallacen Najeriya.

Fadolapo ya jaddada cewa, tallace tallace sana’a ce da ta shahara kamar likitanci, shari’a, lissafin kudi da dai sauransu, tsarin tallan yana karkashin dokar APCON a sashe na 1 da 17 na dokar ta. Kuma laifi ne kowa ya yi talla ba tare da an yi masa rajista da APCON ba.

Ya ce saboda haka majalissar za ta daukar ma matsalar mataki.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *