Wasu Yan Achaba Sun Cinna Ma Rukunin Gidajen Zamani Wuta A Abuja.
Yan achaba sun cinna ma wasu gidaje wuta dake unguwar Lokogoma a Abuja domin daukar fansa kan mutuwar wasu ‘yan uwansu biyu.
Jaridar VANGUARD ta ce, Sama da yan achaba 100 dai ne suka kai hari a rukunin gidaje na Same Global Estate dake yankin Lokogoma jiya Lahadi bayan da aka ce wani direban mota ya kade yan achaba 2 ya ruga da gudu domin tsira.
Akwai dokar hana zirga-zirga a hukumance kan masu tuka baburan haya a mafi yawancin sassan birnin Abuja ciki kau har da babban titin Lokogoma.
Mazauna yankin sun ce yan achabar sun kona gidaje biyu a lokacin da suke kokarin kama direban motar da ya kade masu yan uwa.
A lokacin da Manajan rukunin gidajen Mr. Adebisi Adelowo yake magana a kan lamarin ya ce; “Sama da yan achaba Hausa 100 ne suka kai hari a yankinmu ‘yan sa’o’i da suka wuce, inda kuma suka yi kokarin kona mana gidaje.
“Sun ja kofar shiga gidajen suka kama jifar mutanen ciki. Kuma muka kasa hana su sai da ‘yan sanda da sojoji suka shiga tsakani.
“Daga baya mun samu labarin cewa, sun kai hari a yankinmu ne saboda wasu abokan hayarsu guda biyu da wani direban mota ya banke ya ruga yankinmu domin tsira da ransa saboda binsa da suke yi.
“Mutumen da aka biyo da ba mazaunin gidan bane dai, ya ruga cikin gidajen duba da ofishin ‘yan sanda a gaban gidan.”
