Wata Akanta Mai Shekaru 47 Ta Kashe Kanta A Lekki.
Wata akawun mai shekara 47, mai suna Afolake Abiola ta kashe kanta ta hanyar shan maganin kashe kwari.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 27 ga watan Mayun 2022, a gidanta, mai lamba 1 dake Abayomi Kukomi kusa da Osapa London, Lekki.
Jaridar Vanguard ta bada rohotan cewa, Afolake wadda bata taba haihuwa ba, ta sha fama da bakin ciki na wani dan lokaci kafin ta kashe ta.
“Ta jima tana fama da baƙin ciki saboda bata da miji da yaya.” inji dan uwanta.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Lagos, SP Benjamin Hundeyin, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Mayun 2022.
Lokacin da ’yan sandan suka isa wurin, ‘yan uwanta suna wurin, inda suka bukaci a bar musu gawar domin su samu damar binne ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Kuma aka basu damar yin zana’idarta.
