November 18, 2026

Kayyade Cirar Kudi Banki: Za Mu Dauki Matakan Da Suka Dace Kan CBN – Kungiyoyin Arewa.

0

Gamayyar Kungiyoyin Arewa ta sha alwashin daukar mataki kan Babban Bankin Najeriya kan manufofinsa na baya-bayan nan game da kayyade cirar kudade a bankuna.

Babban bankin ya umurci dukkan bankunan da su tabbatar da cewa, kudaden da daidaikun mutane da kamfanoni ke cirewa, bai wuce N100,000 da N500,000 ba, duk mako.

Babban bankin ya kuma ba da umarnin cewa Naira 200 kawai za a rika shigarwa cikin injinan cirar kudi (ATM) na bankuna.

Sai dai Kakakin gamayyar kungiyoyin Abdul-Azeez Suleiman, a wani taron manema labarai a Abuja, ya ce an bullo da wannan manufar ne domin gurgunta ‘yan kasuwan Arewa.

Suleiman ya bayar da hujjar cewa manufar ta sabawa dokar halatta kudaden haram ta 2022 sashi na 2, wanda ya ambato yana cewa ‘Babu wani mutum ko wani kamfani da zai karbi tsabar kudi da ya wuce N5,000,000 ko kwatankwacinsa, ko N10,000,000 ko makamancinsa inba da hanyar bankuna ba a wajen wani kamfani.’

“Don haka gamayyar kungiyoyin sun kuduri aniyar daukar wasu mataka da suka dace don hana Emefiele da babban bankin Najeriya ci gaba da aiwatar da wannan sabon tsari da ke nuna rashin daidaiton kudi na gwamnati, inji majiyar Popular News Hausa ta Sunnews.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *