An Kashe Wata Mata Mai Juna Biyu Yayinda Ake Kokarin Garkuwa Da Mijinta A Borno.
Wata mata mai juna biyu, Misis Mary Barka ta mutu a lokacin da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne ɗauke da bindigogi kirar gida da aka ƙera a Awka suka mamaye kauyen Pelachiroma da ke cikin karamar hukumar Hawul a jihar Borno.
Waɗanda ake zargin, tuni Shugaban mafarauta, Mohammed Shawulu Yohanna, ya kama su, tare da mika su ga jami’in ‘yan sanda na shiyyar Hawul, Habila Lemaka.
A cewar Yohanna, shugaban ‘yan banga/mafarauta a wata hira da ‘yan jarida a wannan Litinin ɗin, an samu rahoton faruwar lamarin ne kwanaki kadan da suka gabata, bayan wadanda ake zargin sun kai hari kauyen kuma suka yi yunkurin yin garkuwa da su, amma ba su yi nasara ba, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard.
