September 18, 2026

Hukumar Yaki Da “Yan Bangar Siyasa da Shaye – Shaye ta Tarwatsa Ofishin Siyasa a Zamfara

0

Daga Hussaini Ibrahim

Kumar yaki da bangar siyasa da shaye -shaye da kuma miyagun ɗaibi’u ƙarkashin jagorancin kwamandan hukumar Bello Muhammed Bakyasuwa ta tarwatsa ofishin ‘yan bangar siyasa da ke kusa da gidan gwamnatin jihar Zamfara da ke Gusau.

Kwamandan hukumar ne ya bayyana haka jim kaɗan da tarwatsa ofishin siyasa a lokacin da ya ke amsa tanbayoyi manema Labarai a ofishinsa da ke Gusau.

Kwamandan hukumar Bello Bakyasuwa ya bayyana cewa, dokar da ta yi hukumar ita ce ta bamu damar yaki da ‘yan bangar siyasa da masu shaye -shayen miyagun kwayoyi da munanan ɗabi’u wannan dokar ce ta ba su damar tarwatsa ofishin ‘yan bangar siyasa na jami’yyar APC da suka samesu da laifuka daban-daban na ta’addanci ,da makamai da suke amfani da su wajan bangar siyasa.

Kwamanda Bakyasuwa ya ƙara da cewa dokar da ta samar da wannan hukumar ta samar da ita ne dan magance matsalar taɓarɓarewar tarbiyar matasa da kuma yakar masu bangar siyasa da ɗaukar makami komai ƙanƙantar sa a lokacin yakin neman zaɓe na kowace jami’yya da ke cikin jihar Zamfara.

Akan haka ne Kwamandan ya yi kira ga Malaman addini da sarakuna da masu hannu da shuni da su taimamawa hukumar wajan ganin ayyukan ta sun samu nasara a cikin jihar ta Zamfara.

A ƙarshe kwamandan ya yi kira ga ‘yan siyasa da matasa da kadda su yarda wasu miyagun ‘yan siyasa su yi amfani da su wajan bangar siyasa da ɗaukar makamai a lokacin yakin Neman zaɓe dan duk wanda suka kama lallai zai yabawa aya zakintai domin a cewar sa zai gamu da fushin hukuma.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *