September 18, 2026

Gwamnatin Najeriya Ta Amince Da Sabon Kudurin Dokar Masu Kwarmata Bayanan Sirri.

0

Majalisar zartaswa ta Gwamnatin Najeriyar dai ta koka kan yadda tsarin masu kwarmata bayanan sirrin da gwamnatin tarayya ta kaddamar a ranar 21 ga watan Disamba, 2016 ya taɓarɓare.

Tsarin da aka yi a karkashin Ma’aikatar Kudi ta gwamnatin Najeriya, ya nemi jama’a su rika kwarmata bayanan da suka shafi ayyukan zamba, cin hanci, kudaden gwamnati da aka sace, almundahanar kudade, bada labarin kadarorin gwamnati, dama duk wani nau’i na almundahana ko sata ga hukumomin dake yaki da hakan. Har ila yau, tsarin ya yi albishirin kudin lada ta 2.5 – 5 na kudaden da aka kwato ga dukkan wanda ya bada labarin da aka samu nasarar kwato kudaden da aka yi awom gaba da su.

Ministar kudin Najeriya Zainab Ahmed, a wani taron manema labarai jiya a Abuja, bayan kammala taron majalisar zartaswa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta, ta ce gwamnati ta lura da yadda tsarin kwarmata bayanan sirrin ya lalace, saboda mutane na fargabar yin hakan gudun jefa rayuwarsu cikin hadari.

Ta ce domin karfafa yaki da cin hanci da rashawa, majalisar ta amince da wani sabon kudirin doka wanda zai kare masu fallasa bayanan da gwamnati za ta yi amfani da su.

“Ma’aikatar kudi ta gabatar da wasu abubuwa a ranar. Kuma na farko shi ne kudirin dokar masu kwarmata bayanan sirri na shekarar 2022. Majalisar ta yi bita akan hakan don tabbatar da ya yi daidai da dokar bada shaida.

“Dalilin amfani da tsarin kwarmata bayanan sirri shi ne don ƙarfafa yaƙi da cin hanci da rashawa, tare da bada kariya ga mutanen da zasu riƙa kwarmata ma gwamnatin bayanan.

“Kamar yadda kuka sani, majalisar ta amince da kafa kwamitin binciken kudade na gwamnatin tarayya mai laƙabi da PICA. Kwamitin dai na yin haɗin gwiwa da hukumar EFCC, ICPC, DSS, NFIU da kuma ofishin ministan shari’ar Najeriya.

“Mun lura cewa, masu kwarmata bayanan sirrin sun ja baya. Mun tsunduma ayyuka a shiyyoyin Najeriya 6, ɗaya daga cikin abubuwan da aka fahimta kuma shi ne masu bada bayanan na tunanin haɗarin da zasu iya shiga sakamakon bada bayanan sirrin. Saboda haka, kudirin dokar masu bada bayanan sirrin ya maida hankali wajen sirranta bayanan masu aikin kwarmaton, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Sunnews.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *