2023: Dattawan PDP Sun Ɓullo Da Sabon Salon Amsar Mulki A Zamfara
Daga Hussaini Ibrahim
Shugaban kwamitin dattawan jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara Alhaji Salihu Mai-Buhu Gumi , wanda ya samu wakilcin sakataren kwamitin dattawan jam’iyyar PDP na jihar Zamfara Inginiya Ibrahim Agege, ya ce jam’iyyar a karon farko ta shirya tsaf domin sauya salon lashe zaben da amshe mulkin jihar daga hannun jam’iyyar APC zuwa PDP.
Sakataren ya bayyana hakan ne a yau yayin da yake zantawa da manema labarai a Gusau, babban birini jihar Zamfara.
“A cewar sa, jam’iyyar PDP ba ta taba kafa gwamnati ba a tarihin zabukan jihar Zamfara, amma a wannan karon insha Allah sun shirya tsaf domin karya lagon jam’iyyar APC dake mulkin.
Ya ce akwai shaidu da dama da ke tabbatar da cewa, al’ummomin jihar sun koka da yadda jam’iyyar APC ta kawo tabarbarewar al’amura, musamman ma rashin tsaro da ke kawo cikas ga ci gaban jihar.
Sakataren ya bayyana yaƙin neman zaben jam’iyyar PDP a matsayin wanda ke cike da zaman lafiya, inda ya ce za a ci gaba da daƙile duk wani nau’in matsaloli, kashe-kashe da daure ‘ya’yanta da jam’iyyar APC mai mulki ke yi, kamar yadda al’ummomin jihar ke zuba ido ba tare da cewa komai ba.
“Za mu ci gaba da mayar da hankalinmu wajan cigaban Jamiyyar. Abubuwan ta’addancin da ake mana a cikin jihar mun bari ga Allah. Jam’iyyar PDP ta himmatu sosai wajen aikin ceto jihar daga matsalar da ke faruwa a cikinta da kowa ke gane ma idanunsa, inji shi.
A halin da ake ciki kuma, ya ce jam’iyyar ta kafa kwamitin dattawa sittin da bakwai (67) da za su zama membobin kwamitin ba da shawara da zai jagoranci jam’iyyar don sake gyara tattalin arzikin jihar domin samun ci gaban da ya dace, tare da fitar da dabarun da za su bi wajen samun nasarar zaben jam’iyyar a shekarar 2023.
Agegeya ya bayyana cewa, mambobin kwamitin sun haɗa da tsaffin shugabannin jihar Zamfara, tsaffin gwamnonin jihar, sanatoci, ‘yan majalisar wakilai, ministoci da kuma masu rike da mukaman jiha ko kasa baƙi daya.
