Ina Amfanin Hana Masu A daidata Sahu Hawa Manyan Titunan Kano?
Menene hikimar Ɗaukar matakin hana masu a daidaita Sahu na jihar Kano hawan manyan tituna daga gobe laraba.
Rahotanni daga jihar Kano da ke arewacin Najeriya na cewa jihar ƙarƙashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje zata haramtawa masu haya da a daidaita Sahu bin manyan titunan birnin Kano.
Wannan batu dai na zuwa ne a daidai lokacin da ita gwamnatin wa’adin ta ke gab da ƙarewa kuma suna san a zaɓi ɗan takarar da suka sanya a matakin ƙasa da kuma jiha baki ɗaya.
Haka kuma fiye da kashi sittin na mutanen Kano na amfani da KEKE NAPEP ko dai zuwa wajan aiki da makaranta da sauran hidimomi na yau da kullum.
Shin irin wannan mataki da gwamnatoci ke ɗauke zaki haifar da ɗa mai ido a daidai lokacin da ya kamata a ce gwamnati na ƙara matsawa kusa da al’ummar ta domin a ci gajiyar juna?
