Buhari Ya Amince Da Sakin Naira 80bn Don Sake Gina Titin Sapele-Benin, Amukpe-Agbor.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da fitar da kudi naira biliyan 80 domin sake gina hanyar Sapele zuwa Benin da kuma titin Amukpe-Agbor-Uromi.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Delta, Sanata Ovie Omo-Agege, ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wata ganawa da mambobin kungiyar Kiristocin Najeriya, da aka gudanar a Sapele, inji majiyar Popular News Hausa ta Vanguard.
A cewar Omo-Agege, ya bukaci gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa da ya san halin da hanyar ke ciki, tun daga cibiyar horar da abubuwan da suka shafi man fetur zuwa Agbor, a lokacin da ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Ya ce hakan ya faru ne saboda ya san an bayar da kwangilar a baya kuma ya bukaci a sake duba ta domin ya sanya ta a cikin kasafin kudin hukumar raya Neja Delta.
Omo-Agege ya yi bayanin cewa “saboda Okowa yana ganin ba zai samu yabo a siyasance ba, lamarin ya lalace.”
