September 16, 2026

Buhari Ya Nemi Majalisar Dattawa Ta halalta Shirye Shiryen Bunkasa Rayuwar Al’umma.

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubutawa Majalisar Dattawa takardar neman halastawa da kuma kafa cibiyoyin bunkasa rayuwar al’umma na NSIP.

Har ila yau, a wannan Talatar ne Buharin ya bukaci a samar da sabbin wuraren shakatawa na kasa guda 10 a fadin kasar nan.

Akan shirye-shiryen tallafa ma rayuwar al’ummar, Shugaba Buhari ya nemi Majalisar Dattawa ta yi nazari tare da amincewa da kudirin dokar bangaren zartaswa da aka gabatar mata a kan haka.

A cikin wasikar da shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ya karanta yayin zaman majalisar, shugaban ya ce yin nazari da kuma amince da kudirin zai samar da dokar da za ta ba da damar aiwatar da shirin yadda ya kamata da nufin kawar da fatara.

Shugaba Buhari ya ce, “Kudirin kafa shirye shiryen tallafa ma rayuwar al’ummar na kasa na neman samar da tsarin doka da na hukumomi don tallafawa da karfafawa talakawa da marasa galihu gwiwa a Najeriya.”

A kan wuraren shakatawa na kasa, shugaban kasar a wata wasika da Lawan ya karanta a zauren majalisar, ya nemi amincewar majalisar dattijai game da umarnin kafa sabbin wuraren shakatawa na kasa guda 10 a fadin Najeriya.

Shugaba Buhari a wasu wasiku guda biyu zuwa ga majalisar dattawa, yana neman a duba tare da amincewa da dokar kafa ɗakunan karatu na kasa ta shekarar 2022.

A cewarsa, dokar da aka gabatar, za ta samar da tsarin doka don kula da dakunan karatu na kasa kamar yadda ake yi a fadin duniya.

Majiyar jaridar Popular News Hausa ta Vanguard ta ce, Bukatar karshe da Shugaban kasa ya yi wa ‘yan majalisar tarayya shi ne nazari da zartar da kudurin dokar hukumar kula da kayan da ake ƙerawa cikin kasa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *