‘Yan Sanda A Zamfara Sun Kama Ɗan Takarar Sanata Na jam’iyyar PDP Tsohon Ministan Sadarwa Hon. Ikira Bilbis.
Daga Hussaini Gusau
Mataimakin Shugaban Jamiyyar PDP na Jihar Zamfara Hon. Mukhtar Lugga ya tabbatar da kama tsohon Minista Yaɗa labarai kuma ɗan takarar Sanata Zamfara ta tsakiya da wasu mutane shida kuma sun baza komarsu na kama wasu daga cikin jiga-jigan PDP a faɗin jihar ta Zamfara.
Hon Lugga ya tabbatar da haka a lokacin da ya ke amsa tanbayoyin manema a Gusau baban birnin jihar Zamfara
Kuma ya ƙara da cewa, gangamin da mu kayi munyi shine da umarnin jami’an tsaro kuma duk inda muka shiga acikin jihar Zamfara jami’an tsaro wasu na gaban tawagar wasu kuma suna baya Inji Mataimakin Shugaban Jamiyyar PDP.
“Ya kuma ƙara da cewa, yanzu haka suna da tabbacin cewa, jami’an suna neman wasu ‘yan jami’yyar PDP ruwa ajalo dan kamu su, idan baku mantaba yanzu haka kusan wata guda ke nan mutanan mu na PDP shida suna gidan Yari da gwamnatin jihar Zamfara tasa aka kama nima nake magana yanzu haka suna farautata” nji Hon. Muktar Lugga.
“Hon Muktar Lugga ya tabbatar da cewa,su babu wani Alon ɗan takara da muka fasa kuma mu jam’iyyar PDP har yanzu duk faɗin jihar Zamfara babu inda muke da allon ɗan takara dan gwamnatin jihar Zamfara ta hana abamu izini sanya Allon tallar “yan jamiyyar mu ta PDP.
Sakataren Kamfendin Sanata Ikira Bilbis da Aliyu Adamu Barmo shima ya tabbatar da kamun tsohon Minista ya bayyana cewa da ya je ofishin C I D da suka kai tsohon ministan da sunan zai amsa tanbayoyi shine suka rike shi. inji Sakatare Bilbis.
