September 18, 2026

Hukumar ICPC Kai Mataimakin kwamandan Civil Defence Kotu Kan Damfara Ta N26.7M.

0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta wato ICPC ta kaii mataimakin kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya ta Civil Defence Edike Mboutidem Akpan kotu, bisa zargin laifin damfarar wasu masu gida ₦26,655,000.

An gurfanar da Akpan ne a gaban mai shari’a V. S. Gaba na babban kotun tarayya dake zamanta a Kwali, Abuja, kan tuhume-tuhume 17, da suka hada da yin amfani da wani kamfani mai zaman kansa da ake cema Danemy Nig Ltd, wajen damfarar masu sayen filaye, inji majiyar Popular News Hausa ta AIT.

Takardar tuhumar ta bayyana cewa, mataimakin kwamandan na gamsar da masu sayen filayen da dadin kunnen cewa, suna hadin gwiwa da hukumar tsaron Civil Defence don biyan wasu makudan kudade na filayen dake Karshi, Jihar Nasarawa da Sabon Lugbe Extension, filin jirgin sama dake Abuja, wadanda ba a ware musu su ba.

ICPC ta shaida wa kotun cewa, laifin da aka aikata tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015 ya saba wa sashe na 19 da 26 (1) (c) na dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuffukan dake da alaka da dokokin shekarar 2000 kuma ana yin hukunci dogaro da sashe na 19 na wannan dokar.

Daga cikin tuhume tuhumen, akwai ina ke zargin Akpan ya yi amfani da damar dake gare ya amshi naira N13,350,000 a shekarar 2011 daga hannun wani mai sayen fili mai suna Igwe Onus Nwankwo a karkashin kamfanin shi da ake cema company Danemy Nig Ltd a matsayin kudaden filaye 10 dake filin jirgin.

A lokuta daban-daban ana zarginsa da karbar N1,305,000 daga hannun Likitoci Robert Okoro da Akuneme Marcel Ikwuoma, don rabon filayen da aka gina a Defenders Family Estate Homes Scheme, filin jirgin sama.

Ana kuma zargi jami’in hukumar Civil Defence din da karbar N2,610,000 daga hannun wani mai suna Chidinma Obasi kan sayen wasu filaye guda biyu da kuma N1,205,000 daga Etuechere Martins, kan wani fili daya.

Wanda ake zargin ya ki amsa laifukan a lokacin da aka karanto masa tuhume tuhumen, inda kuma lauyansa ya roki kotu da ta ba shi beli bisa sharuddan sassauci.

Lauyan ICPC, John-Paul Okwor, wanda bai soki batun neman belin wanda ake karar ba, ya roki kotun da ta bada shi beli bisa sharuddan da suka dace da za su tabbatar da halartar shi a kotu don ci gaba da shari’ar.

Daga nan ne mai shari’a Gaba, ya amince da bayar da belinsa a kan kudi Naira miliyan 5 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.

Kuma dole ne daya daga cikin wadanda za su tsaya masa ya nuna takardun gidansa.

Kotun ta kuma ce, dole ne wanda ake karar ya miƙa fasfo dinsa ga magatakardar kotun.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *