Ya Kamata Gwamna Masari Ya Rika Zuwa Wurin Yan Gudun Hijira Kamar Yadda Takwaranshi Zulum Ke yi — Comrade Bishir Dauda
Daga Auwal Isah
Gamayyar kungiyoyin farar hula sun yi allawadai da abubuwan dake faruwa a sansanin yan gudun hijira dake Jibia, cikin Jihar Katsina.
Sakataren kungiyar Muryar Talaka na kasa kuma kakakin gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar Katsina Comrade Bishir Dauda Sabuwar Unguwar ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar Popular News Hausa.
Kammar yadda ya bayyana, yan gudun hijira ba abinci kadai suke bukata ba, akwai sauran abubuwa da suka shafi ilimi, kiwon lafiya da kuma batun kwantar masu da hankali.
Ya ce gwamnati ce ta kasa ba su tsaro a garuruwansu, har ya kaiga mutanen sun zama yan gudun hijira. Saboda haka ya zama wajibi gwamnati ta bi su har sansanoninsu ta kula da su.
Ya ce badan matsalar tsaro bai tunanin akwai mutum mai hankali da zai bar gidanshi ya koma sansanin yan gudun hijira da zama. Kowa ya sani dukkan inda ake ayyukan ta’addanci dole ne a samu yan gudun hijira”.
Sai dai ya alakanta dukkan wani yanayi da yangudu hijira suke cikin akan matsayar gwamnatin jihar Katsina na kin amincewa da kafa sansanin yan’gudun hijira a jahar duk kuwa da cewa akwai bukatar hakan.
Kwamarad Bishir Dauda ya yi nuni da cewa kamata ya yi gwamnatin jiha ta sake tunanin da take dashi akan batun yan’gudun hijira domin dokar kasa da kasa ta amince a baiwa yan’gudun hijira mafaka da kuma kyautata rayuwarsu kamar sauran al’umma.
Ya kara da cewa kamata ya yi gwamna ya je da kanshi ya ga halinda suke ciki don sanin yadda za a taimaka masu.
Idan dai ba manta ba kafafen watsa labaran Najeriya dana wajenta sun bankaɗo cewa, kimanin mutum 22 sun mutu sakamakon fama da yunwa a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke ƙaramar hukumar Jibiya cikin jihar Katsina.
Sansanin na dauke da dumbin ƴan gudun hijira da suke gudo daga garuruwansu sakamakon karuwar matsalar tsaro a sassan jihar da dama.
Sansanin dai na dauke da akalla mutum 15,000 yawancinsu sun fito daga garuruwan Shimfida, da Zango, da Kwari, da Tsembe, da Tsauni da kuma Mai Wuya.
Rahotanni sun ce garuruwan sun zama tamkar kufai sakamakon hare-haren ƴan fashin dajin.
An bayyana cewa, akwai yara akalla 3,000 a sansanin, baya ga mata da kuma tsofaffi, waɗanda daƙyar da siɗin goshi suke samun abun kai wa ga bakin salati.
Malam Sa’ad Salisu Shimfida shi ne shugaban wannan sansanin ‘yan gudun hijira, ya kuma shaida wa BBC yadda waɗannan Mutunen 22 suka rasa rayukansu sakamakon fama da uƙubar yunwa.
Ya ce “akwai matsalar ruwan sha, ƙarancin abin shimfida, da yawa ma a ƙasa suke kwana, gashi babu maganin sauro da na ƙwari duk babu. Haka kuma ga sarin macizai”.
Dangane da wanan batu BBC ta tuntubi shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Katsina, Alhaji Babangida Nasamu wanda ya musanta zargin.
Kuma yana mai bayyana cewa, “Ni da ma’aikatanmu na SEMA mun mayar da Jibia kamar gida, kusan ko yaushe muna can, kuma kullum muna magana da shugaban ƙaramar hukumar,”.
Ya ƙara da cewa a yanzu haka gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya ba da miliyan 100 don a tsugunar da ƴan gudun hijirar, kuma ana wadata su da abinci sosai.
