An Kama Fasto Da Matar Shi Bayanda Mutane 3 Suka Mutu A Coci.
Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta tsare wani Fasto mai suna Taiwo Olaniyi mai shekaru 48 da matarsa Kemi mai shekaru 28 bisa mutuwar wasu mutane uku a cocinsu lokacin ibada.
Mamallakin Cocin Cherubim da Seraphim dake Osogbo dai yana da cibiyar warkar da marasa lafiya a cikin cocin. An kuma bada rohoton cewa an kai wata Rasheedat Mufutau mai shekaru 58 zuwa coci saboda tana da ciwon suga kuma ta rasu. Haka kuma, wata mata mai suna Anifowose Basira mai shekaru 48 da wani yaro dan wata tara mai suna Abdul-Rahman Afolabi sun rasu a cocin duk a cocin, inji majiyar Popular News Hausa ta Sunnews.
Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar, Yemisi Opalola, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce lamarin ya faru ne a ranar 28 ga watan Yuni.
Ta bayyana cewa, an kama mutane uku dangane da lamarin, amma an saki ɗaya bayan an gano memban cocin ne.
