September 18, 2026

EFCC ta gurfanar da Stella Oduah a kotu kan badaƙalar naira biliyan biyar

0

Daga Ibraheem El-Tafseer

Hukumar Yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arziƙin Najeriya Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da tsohuwar ministar sufurin jiragen sama ta Najeriya Stella Oduah, tare da wasu mutum takwas a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa zargin almundahanar kuɗaɗe.

An gurfanar da mutanen ne kan zarge-zarge 25 da suka haɗa da halasta kuɗin haram, da haɗin baki, tare da amfani da wani asusun ajiyar banki marar suna a bankin First Bank da aka samu kimanin naira biliyan biyar a cikinsa.

Sai dai bayan karanto musu zarge-zargen Oduah tare da sauran mutanen takwas ciki har da wata tsohuwar hadimarta, sun musanta duka zarge-zargen da hukumar ke yi musu.

Alƙalin kotun, Mai shari’a Inyang Ekwo ya umarci ofishin babban Atoni-Janar na ƙasa da ya karɓi hurumin shigar da ƙarar daga hannun hukumar ta EFCC.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *