An Kai Fasto Gidan Kaso A Ondo Saboda Sata.
An daure Friday Okeneji, shugaban Cocin Christ Apostolic Church (CAC) da ke Ona Iwa-Mimo, Iwaro Oka Akoko, a jihar Ondo, tsawon shekaru biyu.
Kotun majistare da ke zamanta a Oke Eda a Akure ta yanke wa Okeneji hukunci ne a ranar Laraba 12/07/2023 bayan da aka same shi da fasa wani shagon kayan sinadarai, ya saci kayan da suka kai na Naira 130,000, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta bayyana.
Rahotanni sun bayyana cewa, wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 2 ga watan Yuli, 2023, a Iwaro Oka Akoko.
Da ya bayyana a gaban kotun, faston ya amsa laifuka biyu da kotun ta karanta a gabansa.
Ya amsa cewa ya aikata laifukan ne da nufin yin amfani da kudaden wajen biyan kudin jana’izar mahaifiyarsa da aka shirya yi a watan Agusta.
Alkalin kotun, Damilola Sekoni, wanda ya yanke wa Fasto Okeneji hukunci kan tuhume-tuhume biyu, ya ce zai gudanar da zaman gidan yari ko zaɓin biyan tarar N100,000.
Sekoni, ya shawarci wanda aka yankewa hukuncin da ya sake hali, kuma ya yi koyi da kyawawan halaye na Kirista yayin da yake zaman gidan yari.
