September 18, 2026

Bakuwar Cuta Ta Kashe Mutane 5 A Jihar Kaduna, An Kwantar Da 10 Asibiti.

0

Rahotanni sun bayyana cewa mutane 5 ne suka mutu sannan sama da 10 aka kwantar a asibitin tunawa da Sir Patrick Yakowa da ke garin Kafanchan sakamakon barkewar wata cuta da ba a sani ba a garin Kafanchan da ke karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta bayyana.

Wadanda aka bada rohoton cewa sun mutu sakamakon barkewar ya zuwa lokacin haɗa wannan rohoton sun haɗa da Zulaihat Abdurrasheed (13), Hussaina Aliyu (13), Maryam Mustapha (3), Aliyu Umar (4), Abdulshakur Umar (2) da ke da wannan shekarun.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar Dailytrust, sakataren asibitin, Ezra Joshua, ya ce asibitin ya dauki samfurin awonsu zuwa Kaduna don tabbatar da nau’in cutar da maganinta.

Jaridar Dailytrust ta gano cewa, hukumomin makarantun renon yara da na Firamare da ke Kafanchan sun kulle su, bayansa suka aika dalibansu gida sakamakon samun rahoton bullar cutar a ranar Laraba.

“Eh, mun samu rohoton bullar sabuwar cutar da ke farawa da zazzabi, ciwon kai, ciwon makogwaro da sanyin jiki gaba daya da ke shafar yara ‘yan shekara 13 zuwa ƙasa. Mun samu labarin cewa tuni yara hudu zuwa biyar suka mutu a garin Kafanchan, amma ba za mu iya tabbatarwa tun da ba a zo wurinmu ba. Abinda ke akwai shi ne mun killace mutum 10, kuma an kai samfurin su Kaduna a halin yanzu” inji shi.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *