Zulum Ya Iske Asibiti Cikin Duhu A Daidai Lokacin Da Ya Kai Ziyarar Ba Zata.
Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya nuna rashin jin dadinsa kan rashin wutar lantarki da kuma wani yanayi da ya iske babban asibitin garin Gwoza.
Zulum wanda ya kai ziyarar aiki ta yini ɗaya a Gwoza, ya kwashe darenshi a garin da ke zama hedikwatar karamar hukumar Gwoza a kudancin Borno.
Gwamnan, wanda ya saba kai ziyarar ba-zata a cibiyoyin gwamnati a kokarinsa na gane wa idonsa abubuwan da ke faruwa, ya je asibitin ne cikin daren ranar Asabar.
Zulum ya zagaya domin gane ma idonsa asibitin.
“Ba abin amincewa bane a ce cibiyar kiwon lafiya kamar babbar asibitin Gwoza tana rasa muhimman abubuwan more rayuwa kamar wutar lantarki. Wannan abu ya shafi ingancin kula da marasa lafiya da kuma kwarewar malaman kiwon lafiya, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Sundaytrust ta bayyana.
