Hukumar DSS Ta Kai Emefiele Gaban Kotu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar DSS Peter Afunanya ya fitar ranar Alhamis, ya ce an kaiEmefiele kotu ne bisa bin umarnin kotu.
Hukumar ta bayyana cewa ta gurfanar da dakataccen gwamnan babban bankin Najeriyar Godwin Emefiele a gaban kotu, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta Premiumtimes ta bayyana.
Jaridar Premiumtimes ta ruwaito yadda babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Alhamis, ta umurci hukumar DSSS da ta gurfanar da Emefiele a kotu ko kuma a sake shi bayan da ya shafe makonni da dama ana tsare da shi.
Sanarwar Afunanya, wacce aka saki sa’o’i bayan umarnin kotu, ba ta bayar da cikakken bayani kan tuhumar da ake yi wa Emefiele ba ko kuma kotun da ake tuhume shi.
“Bayan umarnin wata babbar kotun Abuja a ranar 13 ga Yuli, 2023, hukumar tsaron ta DSS ta tabbatar da cewa an gurfanar da Godwin Emefiele a gaban kotu bisa bin umarnin,” kamar yadda Afunanya ya bayyana.
“A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Peter Afunaya, ya fitar, ya tuna cewa, a shekarar 2022, hukumar ta nemi umarnin kotu don ta tsare shi akan wani bincike da ake yi.
“Sanarwar ta yi nuni da cewa koda cewa Emefiele ya samo umarnin hana a kama shi daga babbar kotun birnin tarayya Abuja, amma hukumar ta kama shi ne a watan Yuni, 2023, bisa sabbin tuhume-tuhumen da ake zarginsa da aikatawa, wanda daya daga cikinsu ya zama tushen gurfanar da shi a halin yanzu.
“Hukumar ta tabbatar wa jama’a cewa, zata nuna ƙwarewa, da adalci wajen tafiyar da ayyukanta daidai da tanadin doka,” in ji kakakin.
