Tinubu Ya Bayyana Dokar Tabaci Akan Abinci.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kafa dokar ta-baci akan abinci a kasar.
Dele Alake, mai magana da yawun shugaban kasar ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar.
Shugaban ya ba da umarnin a sauwaƙa dukkan wani abu da ya shafi abinci da samar da isasshen ruwan sha duba da mahimmancin su ga rayuwar dan adam a cikin majalisar tsaro ta (NSC), kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta bayyana.
Wannan umarnin na cikin kudurin gwamnatin Tinubu na ganin an tallafa wa masu karamin karfi.
Alake ya ce shugaban kasar ya damu da tsadar kayan abinci da kuma illar hakan ga yan kasa.
Shugaban ya kuma ba da umarnin a gaggauta sakin taki da hatsi ga manoma da magidanta domin rage radadin cire tallafin mai.
“Dole ne a yi haɗin gwiwa cikin gaggawa tsakanin ma’aikatar gona data albarkatun ruwa don tabbatar da yin noman rani da kuma tabbatar da cewa ana samar da abinci kowace shekara.”
“Ya kamata mu ƙirƙira tare da taimakama ma hukumar kula da kayayyaki ta ƙasa wacce za ta yi nazari tare da ci gaba da tantance farashin kayan abinci da kula da dabarun adana abinci wanda za a yi amfani da shi a daidaita farashin hatsi da sauran kayan abinci. Ta hanyar wannan hukumar, gwamnati za ta daidaita hauhawar farashin kayan abinci,” in ji shugaban.
