September 18, 2026

Kwara: EFCC Ta Kama Yan China 13 Masu Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba.

0

Jami’an shiyyar Ilorin na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC sun kama wasu ‘yan China 13 bisa zargin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar Kwara.

Wadanda ake zargin, sun haɗa da mace ɗaya da maza 12, kuma an kama su ne a ranar Laraba 12/07/2023 a GRA da ke Ilorin, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta bayyana.

Hukumar ta ce hakan ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri game da ayyukan da suke yi na hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da kuma rashin biyan hakkokin gwamnatin tarayya kamar yadda doka ta tanada wanda ya sabawa sashe na 1 (8) (b) na dokar laifuffuka daban-daban na M17, 1983.

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce bincike kafin kama su ya nuna cewa masu gudanar da aikin na da wuraren hakar ma’adanai daban-daban a kusan dukkanin kananan hukumomin jihar 16.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *