Hukumar Bunƙasa Kiwon Lafiya Ta jihar Katsina ta ƙaddamar Da Kwamitin Bada Shawarwari Kan Kiwon Lafiya a Shiyyar Funtua.
Daga Awwal Isah, Katsina
Shugaban hukumar Dr. Shamsuddeen Yahaya ya ce kwamitin zai ba al’umma damar shiga cikin al’amuran da suka shafi lafiya.
Kamar yadda ya ce, matakin hakan zai rage dogaro kan gwamnati, tare da ba al’umma damar bada gudunmuwa wurin cimma abinda aka sanya gaba.Shugaban hukumar ya bayyana cewa, jami’an kwamitin za su riƙa bada shawara, tare maida hankali wurin ciyar da al’amuran cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na K/Hs gaba.
Da yake magana, daraktan sashen mulki na hukumar Dikko Bala Kofar Sauri ya hori kwamitin da a koda yaushe ya riƙa bibiyar sha’anin kiwon lafiya na al’umma don bada rohotan abinda ke faruwa ga hukumar don ɗaukar matakin da ya dace.
Ya kuma yi kira ga membobin kwamitin da su maida hankali don samun nasara ga kwamitin.Shima da ya ke magana a madadin shuwagabanni mulkin ƙananan Hukumomi 11 na shiyyar Funtua, shugaban mulkin karamar hukumar Funtua Hamza Sabuwar Ƙasa ya bayyana kafa kwamitin a matsayin abun ci gaba.
Haka kuma a tsokacinshi, hakimin Sabuwa Muhammad Bello da wakilan hakimin Malumfashi Dr. Zayyana Abubakar sun bada tabbacin goyan bayan masu riƙe da sarautun gargajiya ga kwamitin
