‘Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Garuruwa A Safana Sun Kashe Mutun 10 -Hon. A.J Runka
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Rahotanni daga yankin Safana ta jihar Katsina na cewa ‘yan bindiga sun mamaye wasu garuruwa da suke kusa garin Safana tare da kashe da dama da kuma sace dukiyoyin al’umma
Wani mazaunin wani kauye da ya ce mu sakaya sunansa ya shaidawa wakilinmu cewa ‘yan bindigar sun mamaye garin ilaila kusan kwana uku ke nan suna kai hari ba ji, ba gani, kuma ana samu asarar rayuka a wannan kauye.
Haka kuma ya shaida mana cewa ‘yan bindigar sun kai irin wadannan hare-hare a garuruwan Habil da cirena duk a cikin karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, an kuma samu asarar dukiyoyi a wannan harin ta’adancin da suka kai.
Sai dai dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Safana a majalisar dokokin jiha Hon. Abduljalal Haruna Runka ya tabbatar da faruwa wannan al’amari tare fadin cewa lallai jama’ar wannan yanki suna cikin tashin hankali.
“Gaskiya ne wannan al’amari yana faruwa, kuma tuni muka shaidawa hukumomin tsaro domin daukar mataki akan al’amari wanda tuni suma sun daukin matakin da ya da ce domin ganin an shawo kan wannan al’amari” inji shi
A cewarsa bayanin da ya samu, ‘yan bidiga daga jihar Zamfara ne suka kawo harin daukar fansa akan wani tubaben dan bindiga da ke garin ilallai, amma cikin rashin sa’a ba su tarar da shi ba, shi ne suka huce haushi akan jama’a.
“Amma dai maganar da nake da yanzu shi ne, mun sami labarin rasa rayuka goma mata takwas maza biyu a wannan hare-haran da aka kai, kuma mazauna wadanan garuruwa sun shaida mana cewa sun ga jama’an tsaro sun fatataki ‘yan bindigar bayan sanar da su halin da ale ciki.
Wannan yanki dai yana dade yana fama da farmakin ‘yan bindiga kasancewarsa yana da alaka da babar maboyar ‘yan ta’ada da ake dajin Rugu da yake da iyaka da jihar Zamfara da kuma wasu manyar dazuzuka da barayi ke boyewa
Sai dai kuma duk kokarin da muka yi domin ji daga hukumomin tsaro abin ya ci tura, amma dai muna jira jin daga bakinsu domin sanar da al’umma irin matakan da ake dauka akan wannan al’amari
