September 17, 2026

Dubu Sun Taro Wajan Nadin Cigarin Musawa Bala Abubakar Musawa

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Sarkin Musawan Katsina Hakimin Musawa ya nada Alhaji Bala Abubakar Musawa a matsayin cigarin Musawa na daya a fadarsa da ke karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina.

Waton wanda ya zamu halartar dubun dubatar jama’a da suka hada da kusoshin gwamnati ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa ‘yan uwa da abokan arziki sun shaida wannan gagarumin taro da aka gudanar a jiya asabar

Bala Abu Musawa shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina kuma dan kasuwa ne kazalika manomi ne da ya ke da alaka ta mutunta jama’a, wanda ake ganin haka tasa wannan nadi na shi ya zama zakaran gwajin dafi a wannan masarauta.

Haka kuma wannan rana ta shaida wasu nade-nade da hakimin Musawa Alhaji Sagir Inde ya yi tare da na cigarin Musawa, Bala Abubakar cikin tsari da kwanciyar hankali.

Wadanda aka nada din sun hada da Sallaman Musawa, Alhaji Hassan Ibrahim Danhaire, Talban Musawa, Alhaji Abdullahi Aliyu, Cigarin Musawa, Alhaji Bala Abu, Zannan Musawa, Hon Lawal H. Yaro, Tafidan Musawa, Alhaji Sule Musa Rijau da Sarkin Fadan Musawa Alhaji Ahmad Adamu Dankawu.

Sauran wadanda aka nada din sun hada da Alhaji Dalha Danjanku a matsayin Ajiyan Musawa, Alhaji Muhammadu Inuwa matsayin Sarkin Zagi da kuma Alhaji Sani Sa’idu a matsayin Ardon Musawa.

Jim kadan bayan kammala wannan gagrumin nadi, Sarkin Muswan Katsina hakimin Musawa Alhaji Sagir Inde godewa Mai Martaba Sarkin Katsina da ya amince masa nade nade da ya yi, wanda ya ce an yi su cikin nasara. 

Alhaji Sagir Inde ya kuma godewa  wadanda aka nada din da ma dukkan wadanda suka halarci bikin nadin wanda ya ce an nuna kara da karamci.

Har yanzu ‘yan uwa da abokan arziki na cigaba da zuwa gaisuwa ban girma wajan cigarin Musawa Bala Abubakar domin nuna murnarsu da kuma fatan alheri.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *