Kudirin Kafa ‘Yan Sanda Jihohi Ya Samu Cikas A Majalisar Wakilai Ta Tarayya
Daga Awwal Isah, Katsina
Kula da yi ma kudin tsarin mulki gyaran fuska ya samu turjiya ga ƙudurin dokar da ke san kafa ‘ƴan sandan jihohi.
Ƙudurin dokar wanda wani ɗan majalissar wakilan Najeriya da ya fito daga jihar Akwa Ibom Onofiok Luke ya gabatar, ya tsallake karatu na 2 a zauren majalissar wakilan tun cikin watan Yunin shekarar da ta gabata.
Kuma kamar yadda aka sani dai, gwamnatin tarayya ke da ikon bada umarnin kafa doka ta amincewa da jami’an ‘ƴan sanda da ma sauran jami’an tsaro.
To sai dai majalissar dokokin ta yi ƙoƙarin faɗaɗa wannan doka ta 214 (c) domin ba majalissar dokokin ƙasa da ma na jahohi ikon samar da jami’an tsaron ‘ƴan sanda, da ma sauran batutuwan tsaro a matakin jihohi.
A lokacin zaman majalissar na ranar Laraba dai, ƴan majalissu 14 ne su ka jefa ƙuri’an ƙin amincewa da batun, yayin da 11 kuma su ka jefa ƙuri’ar amincewa.
Majiyarmu ta jaridar “The Cable” ta ci gaba da bayyana cewa mataimakin kakakin majalissar wakilan Idris Wase, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin kula da yi wa kundun tsarin mulkin Najeriya gyaran fuska, ya amince a kaɗa ƙuri’a akan kudurin dokar bayan da wani ɗan majalissar wakilai da ya fito daga jihar Bayelsa Fred Agbedi ya gabatar da ƙudurin cewa, a kaɗa ƙuri’a aka batun.
Da wani ɗan majalissar wakilai Muhammad Wudil, wanda shi kuma ya fito daga jihar Kano ke sukar kudurin dokar, ya ce akwai abubuwa da dama da ke tattare da samar da ‘ƴan sandan jahohin.
Ya ce akwai buƙatar a lura da rabe-raben kanun ƙasar nan, kuma gwamnoni ma na iya amfani da ‘ƴan sandan jihohin wurin muzgunawa abokan hamayya.
Amma biyo bayan kaɗa ƙuri’a akan kudurin dokar, yanzu ba sauran cewa an yi son kai akan ƙudurin dokar.
Kuma hakan na zuwa ne ‘ƴan makonni kaɗan da shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya bayyana kafa ‘ƴan sandan jihohi a matsayin hanyar da ba ta ɓulewa wurin magance matsalolin tsaron da ake fama da su a cikin ƙasar nan.
Lokuttan da su ka gabata a baya dai, gwamnonin kudancin Najeriya da sauran ‘ƴan ƙasa sun ta kiraye-kirayen a kafa ‘ƴan sandan jihohi, abinda ya ci karo da tsarin tsaron gwamnatin tarayya.
