Halin Dabbanci Da Magoya Bayan Kano Pilars Suka Nunawa ‘Yan Katsina United
Yadda magoya bayan kungiyar Kallon kafa ta Kano Pilars suka rugurugu da babar motar kungiyar Kallon kafa ta Katsina United a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da magoya bayan kungiyar Kallon kafa ta Kano Pilars suka fahimci ‘yan Katsina United za su zara masu kallo a gidan su.
Idan za a iya tunawa a watanni baya, kungiyar Kallon kafa ta Kano Pilars ta maida filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina a matsayin gidanta, kuma sun riƙa samun goyon bayan magoya bayan kungiyar Kallon kafa ta Katsina United.
Saboda haka ne magoya bayan kungiyar Kallon kafa ta Katsina United ke kira ga hukumar kallon kafa ta Najeriya NPA da ta dauki mataki da ya da ce akan wannan rashin hankali da aka yi wa kungiyar Katsina United.
Yanzu haka na nuni da cewa ba dama a cigaba da taka leda a tsakanin kungiyoyin guda a gida Katsina ko kuma a can Kano tunda irin haka na faruwa.?
An yi kiyasin magoya bayan kungiyar Kallon kafa ta Kano Pilars sun yi wa Katsina United ta’adi na aƙalla miliyan hamsin a wannan farmaki da suka kai.
Tuni dai hukumomin gudanarwa na kungiyar Kallon kafa ta Katsina United suka yi Allah wadai da wannan ɓarna da suka kira rashin hankali da tunani da kuma ƙoƙarin tada zaune tsaye da magoya bayan suke neman yi.
Haka kuma sun bayyana cewa za su kadin wannan al’amari a hukumance domin ganin an ɗauki matakin hana faruwar wannan lamari anan gaba.
