September 17, 2026

Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Shugaban Riƙo Na Jam’iyyar PDP Na Jihar Katsina, Alh. Salisu Lawal Uli.

0

Assalamualaikum

Bayan sallama irin ta addinin musulunci tare da fatan samunka cikin koshin lafia. Ya Ibadar azimi? Allah ya karba mana, amin. Bayan haka ina tayaka murnar samun wannan matsayi na rikon Shugabancin PDPn Jahar katsina a wannan lokaci Mai matukar wahala, tare da fatan Allah yayi maka Jagora, ya baka ikon adalci da sauke nauyi cikin sauki, Amin.

Da farko ina baka hakuri saboda zabar wannan hanya ta budaddiyar Wasika, domin baka shawara da janyo hankali, sabanin inyi maka ita a asirce ko kuma inzo har inda kake in sameka in fada maka, na dauki wannan matakin saboda yanke hanzari ga sauran alumma da kuma kafa hujjah, duk kuwa da cewa kanada kima da mutunci a idona, saboda zamanka abokin Yayana da kuma mutuntani da kakeyi a ko yaushe. Kayi hakuri da Allah.

Yallabai akwai abubuwa guda biyu da kake da su, wanda nikeso na kara jan hankalinka da kayi bakin kokari wajen ganin ka kara karesu, duk da nasan ba zakayi wasa dasu ba, amma a yanzu kasamu kanka cikin wani mawuyanci hali na tsaka mai wuyar da kanada bukatar a tunatar dakai yadda zaka kiyaye wadannan baiwa guda biyu da Allah yayi maka, wato:

“Ilimi da fitowarka daga gidan mutunci” wadannan ba kananan abubuwan alfahari bane, tunda ba kowa Allah yayiwa baiwarsu ba. Yallabai yanzu kana kan wani siradin da idan kayi wasa dasu zasu zama basuyi maka amfani ba, idan kuma kayi amfani dasu, ka guji rudin duniya da neman biyan bukatar wasu yan tsirarun mutane, to tabbas zaka cigaba da cin moriyarsu har abada.

Yallabai yanzu lokaci ne da zaka gwadama mutanen da kake jagoranta cewa kanada Ilimi kuma ka fito daga zuri’ar da keda mutunci kuma tasan darajar mutane.

Kada ka yadda wasu Yan tsirarun mutane su bude maka idon cewa su suka kawoka, domin Mulki na Allah ne, kuma dukkan gwagwarmayar nan da kai akeyinta, hasali ma gidanku gidane da ya bada guddumawa wajen kafa Siyasa a Katsina da Kasa baki daya, saboda haka Babu wani tinkaho da wani zayayi maka akan komai, cikin Siyasa ka taso (wadda ake daidai ba kama karya ba).

Yallabai, ka sani lokaci ne yanzu da ka samu damar da zaka bar Yan Jam’iyya su zabi wanda sukeso a matakin zaben fidda gwani, wanda wannan shine adalcin da idan kayishi ka fita har wajen Allah, kuma akwai yiyuwar PDP na iya cin zabe mai zuwa,.

Amma idan ka biyewa masu san zuciyar da suka kashe PDP tunda aka basu Mulki a 2007 kuma suke cikin yin kama karya har yanzu, to marubuta tarihi zasu tunaka da bakin Biro, kuma PDP zata cigaba da zaman a adawa har abada.

A karshe ina rokon zakaji kuma kayi amfani da amfani da iliminka wanjen tantance daidai da ba daidai ba, kuma kayi adalci saboda zakayi bayani a gaban Allah na dukkan abinda ka aikata komai kankantarsa a ranar da babu wanda zaya iya kareka face gaskiyarka.
Bissalam.

Muha’d Auwal Abba Katsina
Juma’a 15 ga Ramadan 1443AH
15th April 2022

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *