Abinda Yasa Muka Rufe Asibitin Okmos -Gwamnatin Jihar Katsina
Rohotanni da ke zo mana na nuni da cewar, gwamnatin jihar Katsina a ƙarƙashin ma’aikatar lafiya ta jihar ta rufe asibiti mai zaman kanta mai suna Okmos da ke cikin Birnin Katsina.
Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya Dr.Kabir Mustapha shine ya sanar da hakan Jim kadan bayan rufe Asibitin da ke daf da Kofar Kaura.
Kamar yadda ya bayyana, rufe asibitin ya biyo bayan gazawar asibitin na biyan kudaden lasisin gudanar da aiki na shekara-shekara da ake biya a Ma’aikatar.
Jaridar The Fact 24 ta ruwaito cewa, laifuka da aka kama asibitin da su sun hada da rashin Rajistar Hukumar Kula Da Likitoci Ta Kasa(Medical and Dental Council Of Nigeria).
Sauran laifukan sun hada da gazawar asibitin na samar da bayanan marasa lafiya da ke ziyartar asibitin domin duba lafiyar su, gami da rashin dakin shan magani a Asibitin.
Babban Sakataren Dr.Kabir Mustapha ya ce tunda farko sai da Ma’aikatar ta bukaci asibitin akan ta yi Gyare-Gyare akan wadannan laifuka amma hakan ya cimma tura.
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, an bayar da takardar dakatar da asibitin ga Hukumar ta wanda hakan ya yi nuni da rufe asibitin kamar yadda doka ta tanada.
The fact 24
